Siyasar Kebbi: Zargin Adamu Aliero da cin amana da almundahanar dukiyar jama'a ga EFCC ya sa an jefa Sani Dododo kurkuku


Bayan Sani Dododo ya zargi tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Adamu Aliero da aikata almundahanar kudi da cin amanar jama'a da sauransu ga hukumar EFCC. Wannan lamari ya jawo an garkame Dododo a Kurkuku a shekara ta 2007.

A shekara ta 2022, Sani Dododo shi ne wanda ke kan gaba yana gaya wa jama'a a jihar Kebbi cewa Alhaji Adamu Aliero ne jagoran siyasar jihar Kebbi.

Duba da cewa jaridu sun ce Sani Dododo ya kai rubutaccen koke ne kan lamarin ga hukumar EFCC. Tambaya a nan shine ina zancen ya kwana? .

EFCC ta wanke Alhaji Adamu Aliero ne kan zargin da Dododo ya yi masa ko jaye karar aka yi?. 

Abu daya ne jama'a ke tambaya a nan, wanda ake zargi da almundahanar kudi da cin amanar jama'a zai iya zama jagoran jama'ar da ya ci amanarsu?

Duba Labarin da Jaridar Allafrica.com ta wallafa kan lamarin:

"Najeriya: Dododo ya sami yanci cikin tsatsaurar sharudda" 

23 SATUMBA 2007

Shugabanci (Abuja)

By Atang Izang

Alhaji Sani Dododo, mutumin da ake tsare da shi a sakamakon karar da ya shigar kan tsohon Gwamna Adamu Aliero na jihar Kebbi, an sake shi. 

A watan da ya gabata ne Alhaji Dododo ya mika koke ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), inda ya zargi tsohon Gwamnan da almundahanar kudi da cin amanar jama’a da dai sauransu.

Alhaji Musa (an sakaya sunansa na farko), na kusa da Dododo ne ya bayyana wa wakilinmu a wayar tarho game da wannan sabon lamari. An gindaya sharuddan belin da aka bayar a Birnin Kebbi. 

Musa ya nuna rashin jin dadinsa, cewa belin wanda ya hada da bayar da mutum hudu wadanda za su tsaya masa (biyu daga cikinsu dole ne su zama ‘yan majalisar dokokin jihar Kebbi da kuma babban" ma’aikacin gwamnati) an yi rashin adalci, tare da la’akari da cewa wadanda ake tuhuma yana amfani da 'yancin fadar albarkacin baki da tsarin mulki ya ba shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN