Wani dalibin makarantar Polytechnic da ke Ibadan a jihar Oyo, ya rasa ransa yayin da budurwarsa ta sume bayan sun dade suna jima'i.
Marigayin, dalibin National Diploma 2 da aka bayyana sunansa da Oromidayo, ya fito ne daga Sashen Injiniya na Civil Engineering, yayin da masoyinsa, Aramide, kuma tana mataki na ND 2 a Sashen kula da harkokin kasuwanci.
Kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito, masoyan sun tsunduma cikin lalata ne bayan sun dawo daga harabar makarantar. An kuma yi zargin sun yi amfani da kwayoyi don inganta aikinsu na jima'i.
“Yana cikin Faculty dina. Jiya yakamata ace ranar da zamu fara jarabawarmu amma makarantar ta rufe. An yi zanga-zanga jiya; haka shi da budurwarsa suka koma gida. Sun sha miyagun Æ™wayoyi kuma suka fara jima'i. Mutumin ya mutu yanzu uta kuma budurwarsa an Kai ta asibitin Kwalejin Jami’ar,” Inji wani makwabcin marigayin.