Majalisar dokokin jihar Kano ta dage ci gaba da zamanta da aka shirya yi a ranar 16 ga watan Mayu da makwanni uku.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Majalisar Uba Abdullahi ya fitar a Kano ranar Lahadi.
A cewar Abdullahi, kakakin majalisar, Hamisu Ibrahim-Chidari, ya sanar da dage zaman ta hanyar wata sanarwa.
Ibrahim-Chidari ya ce a yanzu ana sa ran majalisar za ta dawo da zamanta da kuma na yau da kullum a ranar 6 ga watan Yuni.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya ruwaito cewa, ba a bayyana dalilin yanke wannan hukunci ba.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI