Yadda mutum bakwai suka mutu a gobara da ta tashi a wani gidan mai a Jigawa


Mutane 7 ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai da ke garin Marke a karamar hukumar Kaugama a jihar Jigawa.

Wakilin isyaku.com a Jigawa ya ce Lamarin ya faru ne a gidan mai na Al-masfa Global Enterprise Nigeria Ltd a ranar Litinin 4 ga watan Afrilu da misalin karfe 6 na yamma. 

A cewar wani ganau, gobarar da ta tashi a safiyar ranar Litinin ta kone wani gini da ke zama shingen gudanarwa da kuma wurin kwana na ma’aikatan tashar.

Ya ce gobarar ta tashi ne a lokacin da suke barci kuma mutane bakwai sun rasa rayukansu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton, tawagar ‘yan sandan ta garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kai gawarwakin da wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Hadejia.

Shiisu ya ce mutane shida ne suka rasa rayukansu a nan take yayin da wani wanda abin ya shafa ya mutu yayin da ake jinya.

Ya bayyana sunayen wadanda suka mutu kamar haka: Nasiru Umar Garki, Abdulkadir Nura, Dahawi Garin Babale, Hamza Adamu, Sulaiman Garin Babale, Idris Adamu Jamaga da Salisu Garin Babale.

Shiisu ya ce ba a san musabbabin tashin gobarar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN