Ministan sharia kuma a Antoni janar na Najeriya Dr Abubakar Malami SAN, ya ci gaba da isar da ayyukansa na jinkai ga alummar Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.
Malami ya isar da gudunmuwarsa na inganta rayuwar jama'a ta hanyar gina riyojin samar da ruwan sha na zamani watau Borehole a wurare da dama.
Wasu daga cikin ayyukan borehole da ya yi sun hada da:
1. Gina borehole a Rafin Zuru. Lamari da ya Samar da sauki tare da share hawayen alummar wannan unguwa wajen samun ruwan sha kamar yadda Malam Ikara Abubakar Adashe, Sarkin Samarin Hausawan yankin Rafin Zuru ya tabbatar mana a lokacin ziyarar gani da ido da shafin labarai na isyaku.com ya kai a wannan unguwa.
2. Gyara rijiyar tuka-tuka a Makarantar Islamiyya na Malam Ahmadu a Unguwar Tudunwada Zuru. Shafin isyaku.com ya samo tabbacin wannan aiki. Kazalika Malam ya ce yana matukar godiya ga Dr Abubakar Malami sakamakon wannan rijiya da ya gyara, wanda ya ce yanzu haka jama'ar Unguwar na dogaro da wannan rijiya domin samun saukin samun ruwa na gudanar da rayuwarsu. Kazalika, shafin isyaku.com ya lura da yadda jama'a suka dukufa wajen amfani da wannan rijiya lokacin da jami'an shafin suka kai ziyarar bazata.
3. Dr Abubakar Malami ya taimaka wa Marayu maza da Mata fiye da sittin da bawai (67) a makarantar Islamiyya na Madarasatul Darul Quran da ke unguwar Sha da Wanka.
Wakilin shuwagabannin wannan Makaranta mai suna Malam Ibrahim Muhammad ne ya tabbatar wa shafin isyaku.com cewa Makarantar ta sami sakon Ministan shari'a Abubakar Malami daga hannun Uwargidarsa Hajiya Aisha Malami lokacin da ta kai masu ziyara.
Daga cikin kayan abinci da ta bayar sun hada da buhunan shinkafa, suga da gero domin ciyar da wadannan bayin Allah yara Marayu.
Malam Ibarahim ya mika godiyarsa ga Dr Abubakar Malami amadadin shugabannin Makarantar.
4. Dr Abubakar Malami ya gina borehole da ke amfani da hasken rana a Makarantar Maahad na Malam Ja'afaru Jibrin.
Kazalika Dr Malami yana taimaka wa Makarantar wajen ciyar da dalibai 536 wanda sun fito daga jihar Kebbi kamar su garuruwan Kola, Zauro, a da sauran wurare irin su Bena, Wasagu da garuruwan jihar Zamfara. Taimkao wajen ciyar da su bisa tsarin jinkai yana is gremu daga Mai girma Ministan sharia Dr Abubakar Malami, Inji Malam Ja'afaru.
5. Dr Abubakar Malami ya gina borehole a Rikoto Ward kusa da Fadar Sarkin Rikoto. Alhaji Abubakar Mai shinkafa, campaign coordinator na Khadimiyya a Rikoto Ward, Zuru ya tabbatar wa tawagar shafin labarai na isyaku.com cewa , kafin Malami ya gina masu wannan borehole, jama'a na cikin mawuyacin wahala na rashin ruwa musamman idan rani ya yi.
Ya ce yanzu kam, ba kawai yan Unguwar ke amfana da wannan borehole ba, har da makwabtan Unguwar na amfana da shi wajen samun ruwa domin amfanin rayuwa.
6. Dr Abubakar Malami ya gina borehole a Unguwar Zango kuma jama'a suna matukar Amfana da shi kamar yadda Isya Umar Maiwada ya shaida Mana. Duk da yake wannan borehole ya sami matsalar da yake bukatar gyara a lokacin da tawagar shafin labarai na isyaku.com ya ksi ziyarar gani da ido.
Maiwada ya ce Dr Abubakar Malami ya bayar da umarnin cewa za a gyara wannan borehole domin jama'a su ci gaba da amfani da shi, duba da matukar tasiri da rijiyar ta samar da sauki ga rayuwar jama'a wajen sha'anin ruwan amfanin yau da kullum.
7. Gyara borehole mai amfani da hasken rana a Unguwar Mahauta a tsohon kasuwa Zuru. Malam Abdulhadi Hassan ya mika godiya ga Dr Abubakar Malami, amadadin al'umman Unguwar, yayin da Malam Abdullahi Mahmud Roro ya kara bayani yadda damar da wannan borehole ya kawo sauki ga jama'ar Unguwar har da makwabtarsu. Ya ce hatta Masallaci da dabbobinsu duk suna amfana da wannan rijiya.
Wasu kenan daga cikin ayyukan taimakon jama'a da Dr Abubakar Malami ya yi wa jama'ar garin Zuru.
Kazalika, mun samo daga majiya mai tushe, cewa Malami ya sa baki kan lamarin albashin ma'aikatan sabuwar Jami'ar koyon aikin gona na Zuru, kuma ma'aikatan sun sami biyan bukata bayan Dr Abubakar Malami ya sa baki.
Wannan kadan kenan daga ayyukansa na taimakon jama'a , cewar wani Hadiminsa.