Kwamishinan Yansandan jihar Kebbi CP Musa Baba, ya jaddada aniyar rundunar yan sandan jihar Kebbi wajen ganin an aiwatar da hidimar Karamar Sallah lafiya kalau a fadin jihar.
2. Hakazalika rundunar ‘yan sanda da sauran Hukumomin tsaro a jihar sun shirya tsaf domin tabbatar da jama'a sun gudanar da bukukuwan lafiya kalau. Don haka ya zama wajibi a yi amfani da wannan kafar wajen fadakar da duk masu son kawo fitina da bata gari da su guji yin duk wani abu da ya sabawa doka, domin an dauki matakan dakile duk wani abu na karya doka da oda. Don haka, ‘yan sanda za su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a kafin bikin da kuma bayan bikin.
3. Hakazalika, rundunar tana buƙatar mafi girman haɗin kai daga jama'a ta hanyar samar da muhimman bayanai masu mahimmanci, ko kuma kai rahoton duk wani wanda ake tuhuma ga ofishin 'yan sanda mafi kusa, don Allah.
SP NAFI'U ABUBAKAR, anipr
JAMI'IN HULDA DA JAMA'A,
GA: KWAMISHINAN YAN SANDAN JIHAR KEBBI".