Kebbi 2023: Malami ya magantu cewa bai shiga cikin tseren masu neman Gwamnan Kebbi ba, duba dalili


Antoni Janar na ƙasar nan kuma ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya musanta rahoton dake cewa ya bayyana sha'awar neman kujerar gwamnan Kebbi, kamar yadda Dailytrust ta rahoto

Rahotun Legit.ng na cewa jita-jita ta fara yawo a kafafen sada zumunta cewa Ministan ya nuna sha'awar gaje kujerar gwamnan Kebbi mai ci, Atiku Bagudu, kuma da safiyar Talata rahoton ya ƙara yawaita.

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa Ministan kan harkokin midiya da yaɗa labarai, Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar a madadin Malami ya musanta rahoton.

Sanarwan mai taken, "Har yanzun ban bayyana shiga takara ba - Malami," ta ce karin haske kan lamarin ya zama wajibi duba da wasu kafafe sun fara yaɗa jita-jitar.

"Gwandu ya ce lamarin ayyana shiga tseren wata kujerar siyasa ba harka ce da za'a yi ta a duƙunkune ba ko wani bangaren kafafen watsa labarai ne kaɗai za su rahoto."

"Rahoton ya samo asali ne daga son asani da kuma ƙosawar masoya da masu goyon baya da suka ƙagara."

"Gwandu ya ce idan lokacin da ya dace ya yi, za su ji daga bakin mai gayya mai aiki da kansa da kuma dukkam kafafe, masu ruwa da tsaki, masoya, mambobin jam'iyya da tawagar magoya baya."

Shin Malami ya nuna sha'awar zama gwamnan Kebbi?

Malami, wanda ɗan asalin jihar Kebbi ne, ya shafe wa'adi biyu a matsayin mamban gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma babban jigon jam'iyyar APC.

Jaridar isyaku.com ya samo cewa a shekara ta 2014, Malami ya janye daga takara ba tare da an yi zaben fidda gwani ba ya barwa Abubakar Atiku Bagudu lamari da ya sa ya zama Gwamnan Kebbi har zuwa yanzu. 

Sai dai kirki, tare da taimakon jama'a da Abubakar Malami tare da uwargidansa Aisha Malami ke yi wa Yan jihar Kebbi da Yan Arewacin Najeriya ya sa dubu dubatan Yan jihar Kebbi na ta kiraye-kiraye cewa ya fito takarar Gwamna a 2023, sai dai Malami bai amsa kiran ba kawo yanzu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN