Hukumar tsaro ta Department of state services DSS, ta gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da masu damfara domin ba sa daukar ma’aikata a halin yanzu.
Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya shaida wa jama’a a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a 29 ga watan Afrilu, cewa hukumar ba ta daukar ma’aikata ta yanar gizo, kuma ba ta sayar da fom din neman aiki ko kuma neman kudi daga masu neman aiki kafin daukar ma’aikata.
Sanarwarsa;
"Hukumar DSD tana son sanar da jama’a cewa ba ta daukar ma’aikata a halin yanzu.
“Har ila yau, tana amfani da wannan damar don sake nanata cewa ba ta daukar ma’aikata ta hanyar yanar gizo, ba ta sayar da fom din neman aiki ko neman kudi daga masu neman aiki (lokacin da kuma idan ta dauka).
“An shawarci jama’a, ta wannan sanarwar, a karo na goma sha uku, da su yi hattara da ’yan damfara da ke sarrafa gidajen yanar gizo na karya da yaudara da aka tsara don su zambace su.
"An shawarci masu sha'awar neman aiki da su yi binciken daukar ma'aikata daga hedikwatar ma'aikata, Abuja, da Dokokin Jihohi, da sauran Formations na kasa baki daya, a yanar gizo."