Ana fargaban mutane da yawa sun mutu yayin da tirela ta fado daga gada ta sauka kan wata mota


Ana fargaban Mutane da yawa sun mutu yayin da tirela ta fado daga gada ta sauka kan wata mota a Ojuelegba

Ana fargabar mutane da yawa masu amfani da hanyar sun mutu bayan wata motar tirela ta fado daga gadar Ojuelegba ta sauka kan wata mota a karkashin gadar.

Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a daren ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, a daidai lokacin da hanyar ke cike da cunkoso.

Jama'a sun taru a wurin yayin da suke jiran isowar taimakon.

Yanzu an dauke motar tirelar da wani k'arane kamar yadda aka gani a bidiyon da shaidun gani da ido suka yada.

Rahotanni sun ce mutane sun mutu kafin tirelar ta iya tashi daga motar.


Previous Post Next Post