An yi wa barawo dukar ajali aka banka wa gawarsa wuta, duba yadda ta faru (Hotuna)


Fusatattun matasa a al'ummar Obot Idim da ke karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar Akwa Ibom sun kashe wani da ake zargi da satar wayar wutar lantarki kuma suka kone gawarsa.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin 18 ga watan Aprilu, a kan hanyar Aka Nnung Udoe yan kilomita kadan daga Uyo babban birnin jihar.

Rahotanni na cewa matasa sun yi wa barayin kwanton bauna ne suka kama daya daga cikinsu. Kazalika rahoton ya ce barayin sun dade suna addabar jama'a da satar wayar lantarki, lamari da ke jefa al'ummar cikin yawan fuskantar rashin wutar lantarki. 
Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN