Duba abin mamaki da Abubakar Malami tare da matarsa suka yi wa jama'a da ya zama abin nuni a Arewacin Najeriya


Abubakar Malami SAN, Ministan sharia kuma Antoni janar na Najeriya tare da mai dakinsa Aisha Abubakar Malami sun ba jama'a matukar mamaki lokacin gangamin taron jam'iyar APC na kasa da aka gudanar ranar 28 ga watan Maris a birnin tarayya Abuja. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.

Wata majiya ta labarta cewa Malami tare da Matarsa sun yyi wa jama'ar jihar Kebbi dubun alhairi bangaren samar da lafiyayyen abinci, ruwan sha da sauran cimaka kuma barakalla.

Kazalika majiyar ta ce jama'a da suka je Abuja wajen taron daga jihar Kebbi sun sami wadataccen kulawa musamman daga uwargidan Malami Hajiya Aisha.

Wani ganau ya ce " Gaskiya Minista tare da Matarsa sun yi wa jama'a hidima da muka dade ba mu gan irinsa ba lokacin taron jam'iyar APC na kasa a Abuja.

Tun farko dai daga nan Birnin kebbi ayarin motocin mu na tare da rakiyar jami'an tsaro, kuma daga tsakiyar ayarin akwai motar daukar marasa lafiya watau Ambulance. 

Ba mota ko daya da ta tsaya a hanya lokacin zuwa Abuja ko dawowa. A gaskiya wannan lamari ya ba kowa sha'awa kuma ya nuna yadda zuciyar Malami take dangane da kulawa ga jama'a .

Kazalika an wadatar da mu da abinci wanda aka dinga fitowa da su domin jama'a. Bayan mun koshi tare da yin tanadi, hatta jama'a da suka zo daga wasu jihohi sun sami wannan abinci da abin sha da Malami tare da Matarsa suka samawa jama'a.

A cikin filin wannan taro, motar daukar marasa lafiya da Malami ya bayar muka zo da shi daga Birnin kebbi da shi ne aka dinga amfani wajen yin zirga-zirgan daukar mutane da suka fuskanci matsalar lafiya a wajen taron." Inji majiyar.

Mun tattaro cewa wannan hidima ya kara daukaja daraja da farin jinin Malami tare da matarsa Aisha a fagen siyasar jihar Kebbi

Jama'ar jihar Kebbi daga lungu da sako na jihar suna ta kiraye-kiraye ga Abubakar Malami cewa ya fito takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN