Sakataren riko na APC na kasa yayi murabus


Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, tuni Akpanudoedehe ya kwashe dukkan kayan sa daga sakateriyar jam’iyyar ta kasa da ke titin Blantyre, Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja.

Duk da cewa ba a san dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar ba nan take, amma an gano cewa matakin nasa bai rasa nasaba da yadda ake tafiyar da jam’iyyar ba, inda wasu gwamnonin suka yi yunkurin tsige shi.

Duk da cewa jami’an jam’iyyar da dama sun tabbatar da cewa Akpanudoedehe ya kwashe kayayyakinsa daga ofishinsa, amma ba su iya tabbatar da ganin wasikar da ke nuna ficewarsa ba, inji rahoton Vanguard.

Shi ma Sanata Akpanudoedehe bai amsa kiran da aka yi masa ba domin jin ta bakinsa game da batun na murabus dinsa.

Legit

Previous Post Next Post