Jarumar ta kuma bayyana cewa tana cika salollinta guda biyar, don haka Allah mai gafara ne, idan ta roke sa cikin kuka zai yafe mata.
Ta kuma bayyana cewa kada masu zaginta su yi mamaki idan aka zo ranar tsayawa a madakata su ga ta wuce aljannah ta barsu a tsaye saboda wannan aibata ta da suke yi.
Ta ce:
“Ka san su mutane basa raina abun magana, basa raina abun zagi. Idan ka yi wa mutum abu ba daidai baa bun da nake tsammani idan mutum yana son ka, ka biyo ni ta DM ka yi mani magana wallahi zan saurare ka. Saboda menene, ai babu wanda baya kuskure, na san ni mai laifi ce kuma ni mai zunubi ce.
“Toh ka biyo ni ta DM ni narigada na gama na barsu da magana, abun gabana nake yi bana kallon abun gaban wani. Duk abun da laifin wani yake yi bana kallon shi nawa na sani. Laifi tudu ne ka take naka ka hango na wani.
“Duk zunubin da zan yi bana hada Allah da wani, bana shirka, ina bin Ubangiji, ina sallolina guda biyar. Wallahi na san shi gafurul-raheem ne. Idan na zauna na yi kuka na roke shi zai yafe mun zunubaina, Zai iya yafe mun.
“Kuma ina nan da uwa a raye, kullun tana yi mun addu’an Allah ya rabani da sharrin masu zagina, kullun tana yi mun addu’a Allah ya tsare ni daga sharrin masharrata, domin su masu zagin sune masharrata.
“Ni bana kallon surutun mutane ban ma san suna yi ba wallahi, ni na riga na dauki wannan a matsayin kaddarata ce. Misali kamar ni da Rahama Sadau, Rahama duk abun da za ta yi sai mutum ya je yana zaginta, kila ma ta fi ka kusanci da Ubangiji. Wallahi abu kadan za ka yi sai ya zama abun surutu, abu kadan zan yi sai ya zama abun surutu, toh na barshi a matsayin kaddara ta ce haka, kuma b azan taba kaucewa kaddara ta ba mai kyau ko mara kyau.
“Duk yadda Allah ya yi ni a haka nagode masa. Su yi surutunsu, su yi zaginsu, ni kuma ina a dakina ina shan ruwan sanyi na maida kai na kwanta. Saboda zagin da suke yi mun wallahi irin wannan zagin sai ka gani ina mutuwa, ina tsaye da ku a madakata, sai ku ga na wuce ku, na tafi na barka saboda kowa ta-kai ta-kai, zagin nan sai an dauko ladanka an bani kuma ko ka ki Allah sai na amsa. Na barka a wajen bincike ni na rigada na wuce, don haka zagi baya kari. Ka taba ji ance zagi ya kashe wani?, wallahi baya kisa don haka kada su daina suyi ta yi.”
Ana yawan yi mun gori da na ki yin aure amma na san Allah bai manta da ni ba - Fati Slow
A wani labarin, fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Fati Usman wacce aka fi sani da Slow Motion ta bayyana cewa mutane na yawan yi mata gori kan rashin yin aure.
A tattaunawar, matar cike da hawaye ta bayyana yadda ‘yan uwa da sauran jama’a suke kyamatar ta, wanda hakan ya sa take rayuwa a kebance fiye da shekaru 10 da suka gabata.
Mystique ta bayyana yadda ‘yan uwanta suka taba zane ta akan halin da take ciki.
Ta hadu da masoyinta na gaskiya
Bayan shekaru 3 da labarin ta ya yi ta yawo, ba masoyi kadai ta hadu da shi ba, har mijin aure ta samu sannan ‘yan uwanta sun dawo gare ta inda ta yi aure a shekarar 2021.
Bayan rungumar halin da take ciki da hannu bibbiyu, matar ta bayyana yadda take alfahari da yadda Ubangiji ya halicce ta a mata-maza.
Yanzu haka ita ce shugaban kungiyar lafiya ta Dynamic Initiative da kuma kare hakkin bil’adama, kungiyar da ke wayar da kai akan jinsi.
A tattaunawar da BBC News Pidgin ta yi da ita kwanannan, Mystique ta ce halin da ta shia a matsayin ta na mata-maza ya nuna mata cewa mutum zai iya samun masoyin shi duk halin da yake ciki.
Ta koka akan yadda ake nuna wa mata-maza rashin tausayi a Najeriya inda tace akwai masu irin halittar ta a kasar nan.
Source:Legit