Da dumi-dumi: An tsige Mai Mala Buni daga kujeran Shugaban APC, duba dalili (Bidiyo)


Gwamna Abubakar Sani Belli na jihar Neja ya zama Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bayan tunbuke Gwamna Mai Mala buni na Yobe.

Mai Mala Buni, wanda rahotanni suka nuna cewa yana kasar Dubai yanzu, ya rike kujerar na tsawon shekaru biyu.

Gwamna Bello daga danewa kujerar matsayin mukaddashin ya rantsar da sabin shugabannin jam'iyyar APC na jihohi a zamansa da sauran mambobin kwamitin rikon kwaryan.

Wannan ya bayyana a bidiyon Sakataren yada labaran gwamnan Mary Noe

Daga cikin wadanda ke hallare a zaman akwai Shugaban matasan jam'iyyar APC kuma hadimin shugaba Buhari, Barista Isma'il Ahmad, Farfesa Tahir, Sanata Yusuf Yusuf na Taraba, dss.

Gwamna Bello a jawabinsa ya yi kira da sabbin shugabannin APC na jihohi su hada kan mambobinsa na jiha kuma su daina rikici tsakaninsu.

Yace:

"Ina taya ku murna kuma Shugaba Muhammadu Buhari na tayaku murna. Ina kyautata zaton cewa idan kuka koma jihohinku, zaku hada kan 'yayan jam'iyya."

"Dan Allah a manta da rikice-rikicen baya, wajibi ne ku hada kan kowa don samun sakamako mai kyau a zaben 2023."

Kalli bidiyon:

https://mobile.facebook.com/watch/live/?ref=watch_permalink&v=338305451410425&_rdr

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN