Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga tsaka mai wuya kan yadda siyasar 2023 zata kasance.
Majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa tsohon dan takaran kujeran shugaban kasan zai bayyana ra'ayinsa game da 2023 nan ba da dadewa ba.
Daily Trust ta ce wani babban jigon Kwankwasiyya ya bayyana mata cewa Kwankwaso na shawarar samar da wata sabuwar tafiya gabanin zaben 2023.
Yace:
"Na san nan da karshen wata ko a farkon Maris, shi (Kwankwaso) da wasu shahrarrun yan siyasa na shirin samar da wata tafiya, amma ba jam'iyya ba,"
Ya ce wasu yan siyasa irinsu Buba Galadima da Suleiman Hunkuyi na bada shawarar samar da sabuwar jam'iyya amma Kwankwaso bai goyon bayan haka.
Ya kara da cewa:
"Ya nada ra'ayin sabuwar jam'iyya ba za tayi karko ba kuma da wuya a samu yin rijista kafin 2023. Saboda haka ake son kafa wata tafiya da za'ayi amfani wajen tattaunawa cikin wata jam'iyya mai ci."
Sanata Rabiu Kwankwaso
Zaben 2023: Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga tsaka mai wuya Hoto: Rabiu Kwankwaso Source: Facebook
Yan bangaren Osinbajo sun tuntubi Kwankwaso
Hakazalika an tattaro cewa wasu yan bangaren mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sun tuntubi Kwakwaso, duk da cewa Osinbajo bai bayyana niyyarsa ba tukun.
Wata majiya mai karfi tace har Shugaban jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yi kira ga Kwankwaso ya koma APC.
A cewar majiyar:
"Tattaunawa na gudana tsakanin Oga da su. Suna son ya dawo APC amma ana shawara kai. Ba a yanke ba."
Source: Legit.ng
================
Daga Jaridar iyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook fFacebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI