Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzkin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke lauyan bogi, Adekola Adekeye, kan laifin kirkiran takardun bogi don damfara.
Kakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Abuja, rahoton NAN.
Ya ce asirin lauyan ya tonu ne lokacin da yaje ofishin hukumar karban belin wani dan damfara.
A cewarsa:
"A ranar 11 ga Junairu, 2022, ya zo ofishinmu na Legas karban belin wani mutumi da ake yiwa zargin damfara."
"Amma asirin Adekeye ya tonu lokacin da jami'ai suka bincike takardun da ya gabatar don karban belin mutumin."
Sun je har gidansa don bincike
Uwujaren yace jami'an EFCC sun garzaya gidansa don gudanar da bincike kawai sai suka tarar takardun bogi na jami'ar jihar Legas.
"Yayinda aka gudanar da bincike gidansa, an gano takardun bogi na tun shekarar 2005," yace.
"Ya yi ikirarin cewa shine mai ofishin “A.A. Emmanuel & Co. Chambers”, da yake amfani wajen damfara kafin a damkeshi, Za'a gurfanar da shi a kotu."
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI