Wani mutumi ɗan kimanin shekara 57, Muhammad Alpha, ya daɓa wa matarsa, Hamsatu, wuka har tace ga garin ku nan a ranar farko ta sabuwar shekara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Lande dake yankin karamar hukumar Gambi a jihar Adamawa.
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, DSP Sulaiman Nguroje, shi ne ya tabatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Yola.
Yace wanda ake zargi, ɗan kasuwa mai aikin tuƙin mota, ya caka wa marigayya matarsa, Hamsatu Muhammad, yar shekara 40 wuka bayan wata ƙaramar taƙaddama ta haɗa su.
Ya ƙara da cewa taƙaddamar da ta shiga tsakanin su ce ta yi sanadin mutuwar auren su, wanda suka shafe shakaru sama da 20 a tare da juna.
Kakakin yan sandan yace a ranar 1 ga watan Janairu, 2022, hukumar yan sanda ta damke direban bisa zargin hallaka matarsa Hamsatu.
A cewar kakakin yan sandan bayanan da suka samu na farko ya nuna cewa bayan rabuwar ma'auratan, matar ta koma wani gida kusa da gidan tsohon mijinta.
Yace: "A kokarinta na gyara sabon É—akinta, matar taje gidan tsohon mijinta ta ciro kofa domin gyara sabon wurin zamanta."
"Abin da ta yi ne ya fusata wanda ake zargin, shi ne yasa ya yi amfani da wuka ya daba wa matarsa kuma uwar 'ya'yansa 8 a kirji."
Sakamakon haka ta samu mummunan rauni, mutane suka yi gaggawar kaita asibiti ma fi kusa, inda aka tabbatar da ta mutu."
Kwamishinan yan sanda na jihar, Mohammed Barde, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin, kuma ya roki mutane su daina É—aukar doka a hannun su.
Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI