Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wani sajan da ke karkashin rundunar, Onatunde Joba bisa zarginsa da rashin da’a,
The Nation ta ruwaito. An gan shi a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta a bige ya yi tatil da giya.
Yanzu haka ana ci gaba da tuhumarsa Jaridar The Nation ta rahoto cewa jami’in hulda da jama’an rundunar, SP Yemisi Opalola, ya ce har yanzu ana kara tuhumarsa.
Opalola ya shaida cewa:
“Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a kokarinta na kawar da dabi’un banza, rashin sanin darajar aiki da rashin dabi’u masu kyau, ta kama wani dan sanda,
Sajan Onatunde Joba wanda bidiyonsa yayin da ya yi shaye-shaye ya yadu.
“Tuni hukumar ta ci gaba da bincike akan sa.”
Rundunar ba za ta lamunci rashin da’a ba
Ya kara da cewa:
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode, ya na amfani da wannan damar wurin daukar matakai akan rashin da’a ga duk wani ma’aikaci mai irin halinsa.”
Rundunar ta ce ba za ta lamunci rashin tarbiyya da zubar da mutunci ba daga wani jami’inta ko kuma mai kokarin shiga rundunar ba.
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI