Abubuwan Da Suka Kamata A Sani Game Da Sabuwar Korona Samfurin Omicron


A kwanakin nan ne aka sake samun bullar sabuwar cutar Korona samfurin Omicron wacce ta bullo daga kasar Afirka ta Kudu.

A yanzu haka dai, sabuwar cutar ta Korona samfurin Omicron ta sa cikin duniya ya duri ruwa. Wanda tuni kasashen duniya suka hana ‘yan kasarsu zuwa Afirka ta Kudu wurin da cutar ta bullo.

Yana da matukar muhimmanci jama’a sus ani cewa, Omicron ba ta da bambanci da sauran samfurin Korona irin su Delta da kuma ta farko wacce aka fara samu a kasar Sin.

Sai dai kuma an bayyana cewa sabuwar kwayar cutar Omicro na da yanayin rikida wanda za ta iya fin sauran samfurin Korona na baya. Sakamakon gwaje-gwajen da kwararru suka gudanar ya nuna cewa da yiwuwar Omicron ta dara kwayar Korona samfurin Dalta hadari tare da zama babbar barazana ga kasashen duniya.

Tuni dai kasashen duniya suka dauki tsauraren matakai ciki har da fara rufe iyakoki da hana zirga-zirga a kasashen da aka samu bulluwar cutar.

Sai dai kuma shugaban bankin raya Afika (AfDB) Dakta Akinwumi Adesina ya bukaci shugabannin duniya kar su tsangwami kasashen Afirka saboda wannan sabuwar cutar Korona ta Omicron wajen hana su gudanar da zarga-zirga a ko’ina a fadin duniya.

Adesina ya bayyana cewa ba a kasashen Afirka ba ne aka fara samun bullar cutar Korona, domin haka ka da a hukunta kasashen Afirka da wannan sabuwar Korona ta Omicro. Ya yi kira ga shugabannin duniya su yi adalci a kan wannan cuta.

An fara gano wannan nau’in cutar ne a Afirka ta Kudu a ranar Larabar makon jiya, inda yanzu haka ake ci gaba da samun masu kamuwa da cutar.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, akwai kasashe sama da 20 da aka samu bullar wannan cuta bayan kasar Afirka ta Kudu wadanda suka hada da Malawi, Misira, Faransa, Switzerland, da Israel. Sauran su ne Botswana da Burtaniya da Germany da Italy da Belgiu da Hong Kong da Eswatini da Lesotho da Mozambikue da Namibiya da Zimbabwe da dai sauran su.

Har ila yau, a ranar Larabar makon nan, Hukumar Yaki da Cututtukan Annoba ta Nijeriya (NCDC) ta tabbatar da samun bullar sabuwar na’uin cutar ta Omicron a karon farko a Nijeriya, tun bayan gano cutar a makon da ya gabata.

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da gwamnatin Nijeriya ke aiwatar da dokar hana ma’aikatan gwamnati wadanda ba a yi wa allurar rigakafin Korona ba shiga ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

A sanarwar da hukumar NCDC ta fitar a shafinta na sada zumunta ta ce wadanda suka harbu da sabuwar nau’in cutar Korona ta Omicron suna cikin matafiyan da suka dawo daga Kasar Afrika ta Kudu a makon da muke ciki.

Sanarwar ta kuma ce duk da cewa mutanen na dauke da kwayar cutar, amma ba su fara nuna alamaun kamuwa da cutar ba, wanda a halin yanzu an garzaya da su asibiti domin ba su kulawa ta musamman. Ta kuma ce an soma neman mutanen da suka yi mu’amala da su.

Hukumar ta NCDC ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabbatar sun kiyaye dokokin yaki da cutar domin hana sake yaduwar annobar Korona karo na hudu.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta dora alhakin bullar sabon nau’in cutar a kan rashin dadaito wajen rarraba alluran riga-kafi.

Ta kuma yi gargadin cewa sabon nau’in cutar zai iya haifar da matsaloli a yankuna daban-daban na duniya.

Hakazalika, bayan batun yarjejeniyar zuba jari da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya yo takakkiya zuwa Nijeriya a kai ranar Larabar nan, ana ganin ziyarar tasa na da nasaba da neman goyon bayan Nijeriya a kan tsangwama da kasashen duniya suke yi wa kasar, saboda bullar cutar.

Bayan ziyarar shugaban kasar Afirka ta Kudu kasa da awanni buyu ne hukumar NCDC ta tabbatar da kamuwar mutum biyu a Nijeriya.

Rahotun Leadership Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN