Al'aurar wani mutum dan kasar Jamus ya fara rubuwa bayan maciji ya sare shi a al'ura lokacin da yake zaune a tukunyar lalura a ban daki.
Mutumin mai shekara 47 wanda lamarin ya rutsa da shi yayin yawon buda ido na Safari a kasar Afrika ta kudu, ya sami kulawan gaggawa daga ma'aikatan aikin lafiya, kuma nan take aka garzaya zuwa asibiti da shi inda aka yi masa alluran kashe dafin maciji.
Sai dai al'aurarsa ta fara rubewa a kasa da awa 3 da saran macijin. Lamari da ya sa aka yi masa aiki na musamman a al'aurarsa kuma komai ya koma dai dai.
Rubuta ra ayin ka