Type Here to Get Search Results !

Motar FRSC ta sami hatsari a Bauchi ta kashe mutum 2 ta rutsa da mutum 14


Mutum biyu sun mutu bayan motar sintiri na Federal Road Safety Corp FRSC reshen jihar Bauchi ta sami hatsari ta
afka wani shago.

Jaridar Punch ta labarta cewa lamarin ya faru ne ranar Juma'a da karfe 12:45 na rana a kusa da tashar mota na Alkaleri da ke kan tagwayen hanyoyi na Bauchi zuwa Gombe.

Kwamandan rundunar FRSC na jihar Bauchi Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa wasu karin mutum biyar sun sami rraunuka sakamakon hatsarin.

Ya ce direban motar ya kamu da wanni rashin lafiya ba zato ba tsammani. Ya ce motar tana kan hanyarta na dawowa ofis bayan gudanar da aikin sintiri. Kwatsam sai direban ya yi ihu yayin da yake tuki, kuma nan take ya suma. Sakamakon haka motar da je ta sami hatsari.

Abdullahi ya ce mutum 14 hatsarin ya rutsa da su, ya ce sun hada da maza guda biyar da mata guda biyar dukansu baligai. Sai yara maza guda biyu da yara mata guda biyu hatsarin ya rutsa da su.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies