Ya yi wa yar uwar shi cikin shege har ta haihu rikici ya barke bayan ya ce zai auri wata yarinya


Yanzu haka rikici ya barke tsakanin wasu tagwaye na miji da mace masu suna Amos da Juliana Kunde a jihar Nassarawa, bayan Amos ya gawa wa Juliana cewa yana shirin yin aure. Shafin isyaku.com ya tattaro.

Wani mai suna Bello Lukman ya ce tagwayen sun rasa iyayensu ne bayan wani harin yan bindigan can baya. Daga wannan lokaci suka fara kwanciya tare. Daga bisani Juliana ta sami juna biyu sakamakon kwanciya irin na aure tare da dan uwanta Amos.

Domin kauce wa bakin mutane da sa ido, sai suka tashi suka koma wani kauye, inda ake masu kallon miji da mata.

Sai dai rigima ya barke ne bayan Amos ya gaya wa yar uwarshi Juliana cewa ya shirya zai auri wata yarinya.

Bayanai sun ce Amos da Juliana sun haifi yara kafin wannan lokaci.

Previous Post Next Post