Rashin kunya da wani direba ya yi a gidan mai a Birnin kebbi zai ba ka mamaki


Wani direban mota kirar Toyota Sharon da safiyar Juma'a, ya nemi tayar da kura ta hanyar rena hankalin jama'a da gangan bayan ya shiga gidan mai da motarsa ya wuce kowa ya je kai tsaye a gaba ya tsaya domin a zuba masa mai a garin Birnin kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

Direban motar wanda aka rubuta "Fagicin boys" a motarsa, ya shigo gidan man AP da ke kan titin E.Haruna a garin Birnin kebbi da karfe 9:20 na safe, kuma kai tsaye ya wuce duk motocin da ke jira a kan layi ya zarce wajen fanfon mai ya tsaya.

Duk da yake wani mai mota da ke kan layi ya kalubalanci wannan direba, sai dai direban ya sake komawa layi na gaba ya tsaya a gaban duk motoci da babura da ke kan layi kuma ala dole aka zuba masa mai kafin wadanda ke kan layi bisa ka'ida.


Wani da muka zanta da shi cikin masu motoci da ke kan layi da bai son mu ambaci sunansa, ya yi zargin cewa ire-iren wannan halin karyawa ba gaba yana yawan faruwa da motoci da ke dauke da wasu alamu da ke da nasaba da wasu Yan siyasa saboda nuna isa da neman yi wa talakawa barazana da iko ba bisa ka'ida ba.

Ya ce hakan na isar da sakon irin salon siyasar uwayen gidansu ne da kuma irin tsari da akidar siyasarsu. Ya ce hakkin jama'a ne su kalubalanci irin wannan hali daga yan siyasa marasa martaba balle tausayin talakawa. 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN