Duba asalin Ɗanƙwairo da halifofinsa na jini da na waje


Fitaccen mawaƙin ƙasar Hausa Alhaji Musa Dankwairo Maradun ya yi tasirin da har yanzu ba a manta da shi ba da wakoƙinsa.


Marigayin ya haifi mawaƙa a gidansa da kuma waje a ƙasar Hausa.


Alhaji Musa Dankwairo da ake kira Sarkin kida makada, girman tasirinsa ne ya sa aka gudanar da taron masana a Jami'ar Bayero da ke Kano a ranar 13 ga watan Satumba daidai lokacin ya cika shekara 30 da barin duniya inda masana adabin baka suka tattauna kan tarihi da rayuwarsa da tasirinsa da kuma gudunmuwarsa.


An daɗe ana nazari tun a matakin digiri na farko da na biyu har zuwa kundin digiri na uku kan waƙoƙin marigayi Alhaji Musa Dankwairo a jami'o'i na Najeriya da sassan duniya.


A wajen taron cikarsa shekara 30 da rasuwa, mashahurin malamin nazarin adabin baka Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau ya gabatar da takardar nazari mai taken "Tarihin Rayuwa da Halifofin Makada Alhaji Musa Dankwairo Maradun 1909-1991)" inda takardar ta yi bayani kan yadda waƙoƙin marigayi Dankwairo suka ci gaba da wanzuwa ga magada na jini da na waje.


Ga takardar nazarin Farfesa Gusau game da Danƙwairo

Takardar ta fara ne da gabatarwa kan asali da tushen waƙoƙin baka na Hausa da kuma irin ayyuka da gudunmuwar da mawaƙan kamar marigayi Dankwairo suka bayar ga al'umma.


A cikin gabatarwar, Farfesan ya yi bayani kan zamaninsa da kuma alaƙarsa da Dankwairo da halifofinsa.


Tun ina ɗan makaranta a 1973 nake ganin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun yana rera waƙoƙinnsa, musamman a fadar Sarkin Kudun Gusau da taron kamun Kifi na Argungu da gidansa na Kayan Maradun ko Maradun da kuma a mazuninsa na Gidan Kano.


Wannan takarda ta yi amfani da hanyar bincike na tattaunawa da ganawa da shi marigayi Makaɗa Alhaji Musa Ɗanqwairo Maradun da ɗansa marigayi Alhaji Garba Ɗanqwairo, Halifa na farko da jikansa Alhaji Muhammadu Ɗanjimma, Sarkin Kiɗan Maradun, Ɗanqwairo na yanzu kuma Halifa na uku.


Akwai kuma mataimakansa irin su Marafan Kiɗa, Alhaji Muhammadu Maigayya. Daga nan na bi sawun wasu ayyuka da manazarta suka aiwatar domin samun ƙarin bayanai.


A dunƙule, wannan muƙala ta kawo bayanai a kan tarihin rayuwar marigayi Makaɗa Alhaji Musa Ɗanwaqiro Maradun, Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun, Jihar Zamfara.


Ta kuma ƙunshi wasu dunƙulallun bayanai game da Halifofinsa guda uku (3) tun daga shekara ta 1991 zuwa yau 2021.


2.0 Tarihin Magabata Ɗanqwairo da Haihuwarsa

Musa Ɗanqwairo da magabatansa sun fito ne daga garin Ɗankadu ta cikin Gundumar Bakura ta Jihar Zamfara ta yanzu.


Mahaifin Ɗanqwairo Usman Ɗankwanagga shi ne ɗan Kaka Maiganga kuma shi ne ya haifi Musa Ɗanqwairo. Usman Ɗankwanagga da zuriyyarsa mutanen Ɗankadu ne da ke cikin Gundumar Bakura, kamar yadda bayanai suka gabata.


Usman Ɗankwanagga manoni ne, mai jajircewa a ayyukan gona. Haka kuma makaɗi na noma ne wanda ya shahara sosai.


Sannan ya gaji kiɗan noma daga mahaifinsa, Makaɗa Kaka Maiganga. Har wa yau kuma Usman Ɗankwanagga ya gwama kiɗan fada da kiɗan noma.


A kiɗan fada ya kaɗa abin kiɗa na kotso ne. A wani ƙauli an nuna wajejen 1914 Usman Ɗankwanagga ya bar garinsa na asali, ya fita neman wani wuri da zai yi noma shi da iyalinsa.


A wannan tafiya ce ya haɗu da Sarkin Maradun, Alhaji Ibrahim I (1903- 1923) a wata gonarsa ta Bazamawa. A wannan haɗuwa ce Sarkin Maradun ya amince ya ɗauki nauyin Usman Ɗankwanagga da dukkan jama'arsa, shi kuma ya zama makaɗinsa.


Daga nan ne Usman Ɗankwanagga ya zaɓi ya zauna Birnin Ƙaya gari mai dausayi da ƙasar noma mai albarka.


Iyalin Usman Ɗankwanagga sun zauna a ƙasar Ƙaya a wani wuri da ake kira Tunga, mai yalwar ƙasar noma.


Bayan da Usman Ɗankwanagga ya tsufa, sai ya yi murabus, aka naɗa babban ɗansa Abdu Kurna Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun, mai amfani da kotso.


2.2 'Yarnunu: Mahaifiyar Ɗanƙwairo 'Yarnunu ita ce mahaifiyar Alhaji Musa Ɗanƙwairo.


Ita kuma 'yar asalin Goran Namaye ce, Bazamfariya ce gaba da baya.


2.3 Makaɗa Abdu Kurna Maradun

Shi makaɗa Abdu Kurna an haife shi ne a garin Ɗankadu, a cikin Gundumar Bakura, Ƙaramar Hukumar Bakura, Jihar Zamfara a yau a daidai shekara ta 1899 bisa ƙiyasi.


Tare da Abdu Kurna ne Usman Ɗankwanagga ya baro Ɗankadu zuwa Tunga ta Birnin Ƙaya, Maradun.


Makaɗa Abdu Kurna ya yi kiɗan noma da na masu Sarauta. Shi ya gaji Halifar Mahaifinsa Usman Ɗankwanagga ta Sarkin Kiɗan Sarkin Muradun.


An naɗa Abdu Kurna a matsayin makaɗa na Sarkin Maradun a yayin da mahaifin nasu Usman Ɗankwanagga ya tsufa kuma ya roƙi a maye gurbinsa na Sarautar Kiɗa da babban ɗansa Abdu Kurna.


2.4 Yanayin Haihuwar Musa Ɗanqwairo (1909)

Yanayin haihuwar Musa Ɗanqwairo ya riski wani hali na ɓurɓushin tasirin da zai zo wa Hausawa da al'ummar Arewa na shigowar Turawan Mulkin Mallaka a ƙarƙashin jagorancin Sarauniyar Ingila.


Duk da saɓanin tarihin haihuwa, an ɗauka an haifi Musa Ɗanqwairo a 1909, jim kaɗan da tsayar da mulkin mallaka na Turawa a 1903.


Haihuwar Musa Ɗanqwairo ta wakana a garin Ɗankadu na gundumar Bakura a yau ta Jihar Zamfara, kafin iyayensa su koma Tunga, Birnin Ƙaya ta gundumar Maradun.


An raɗa wa Ɗanqwairo sunan yanka na Musa.


Shi kuwa Ɗanqwairo wata alkunya ce ake gaya wa Musa bayan da ya kai shekaru bakwai da haihuwa, kuma ya fara sa hannu a harka ta kiɗa da waƙa a ƙarƙashin mahaifinsa Makaɗa Usman Ɗankwanagga.


A cikin mataimakan kiɗa na Usman Ɗankwanagga akwai wani baransa, wani mutum mai murya wasai, mai zaƙi da shiga jiki wanda ake yi wa laƙabi da Ƙwairo.


To sai Musa ya gaji irin wannan murya, shi ne mahaifinsa Usman Ɗankwanagga yake faɗin, 'Ga Ɗanqwairo an mayas' (Gusau, 1996: sh. 104)


Bayanan hoto,

Bishiyar tushen Dankwairo


2.6 Iyalin Musa Ɗanƙwairo


Iyali suturar mutum, iyali suturar gida.


A bisa yanayin zamantakewar bil'adama da Aljannu, cikar ɗa, namiji ko 'ya mace ita ce yadda Allah ya hore musu, ya ba su dama, suka assasa zuriya ta kankin kansu.


Alhaji Musa Ɗanqwairo wanda aka fi sani kuma ake kira da Maradun, ya sami jagoranci na iyaye wajen yin matar farko. A yayin zaman Ɗanqwairo a doron rayuwar duniya bayan matarsa ta fari, ya auri mata da yawa kuma wasu daga cikinsu ne suka haifa masa 'ya'ya har goma sha bakwai.


2.6.1Matan Aure na Musa Ɗanqwairo


Mata waɗanda Alhaji Musa Xanqwairo ya aure a rayuwarsa ta duniya su ne: i) Hauwa Taladan (ii) Hajiya Hadiza (Ikka/Tashikka) (iii) Amina (iv) Tumba (v) Rabi ('Yar Zuma) (vi) Maryam (Amarya) (vii) Hauwa (viii) Maimuna


2.6.2'Ya'yan Alhaji Musa Xanqwairo Maza da Mata


Ga tsarin sunayen ƴaƴaan Alhaji Musa Ɗanqwairo Maradun ta bin ɗakunan iyayensu mata da suka haɗa da:


i) Ɗakin Hauwa (Taladan)


ii) Ɗakin Hajiya Ikka (Tashikka)


a) Muhammadu Ɗanmakaɗa, Dauda na ɗaya (1)


b) Alhaji Garba, Zwacin Kiɗi, Marafa, Daudu (2)


c) Audu Adodo, Wakilin Kiɗa


d) Zulaihat


e) Habiba


iii) Ɗakin Amina


f) Ummaru Ka-ji-Dama (Makaɗin Noma)


g) Amina (Kassu): Tana aure a Maradun


iv) Ɗakin Tumba


h) Sanin Ɗanqwairo, Zakin Murya


v) Ɗakin Maryam (Amarya)


i) Sa'adatu


j) Muhammadu Balarabe


k) Umaru


vi) Ɗakin Rabi'a ('Yarzuma)


l) A'ishatu (Indo)


m) Malam Musa Tunau (Malamin Makarantar Allo)


vii) Ɗakin Hauwa


n) Abubakar, Ciroman Kiɗa


o) Amina, Ige


p) Ibrahim Ɗan'auta


viii) Ɗakin Maimuna


Ba ta Haihu ba


2.7.5 Ƙungiyar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ta Kiɗa


Asalin hoton,


Other


Bayanan hoto,

Marigayi Alhaji Musa Dakwairo (Dama) da Khalifansa Daudun kidi Garba Dankwairo


Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya samar da ƙungiya ta aiwatar da kiɗa mai zurfin tunani wadda kuma ta amsa sunanta.


A wannan ƙungiya Ɗanqwairo shi ne Jagora, kuma yana ba ƴan amshinsa damar yin ƙari da ajewa da sauka da saukar sauka da takidi da rakiya ko karɓeɓeniya, wani bi ma da bayayyeniya, sannan da yin takidi na G/Waqa.


Haka kuma a rera wasu waƙoƙi, Alhaji Musa Ɗanƙwairo yakan tafi da Sanƙirori da wasu hadiman waƙa duk a ƙungiyar kiɗa ta Musa Ɗanƙwairo.


Da kansa Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya nuna yadda yake aiwatarwa da ƙullawa da rerawa da sadar da ɗiya a waƙoƙinsa a wannan ɗa na waƙarsa ta 'Yandoton Tsafe Alhaji Aliyu II, mai G/Waqa:


Shirya kayan faɗa mai gida Tsahe:


Jagora: Duk Makaɗan da at Tsahe nai jam'i,


Hab baƙi ha ƴan gidan su duka,


Ƴ/Amshi: Babu mai shirya waƙa kamat tawa,


Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,


'Y/Amshi: Sai a amsa ma shi ba a ƙara mai,


: In nuk ƙulla waƙa a ƙara man,


: Mu haɗu duk azanci gare mu,


: Shin a a mutum guda za ya radde mu,


: Shirya kayan faɗa mai gida Tsahe,


: Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.


Jagora: Ga mu hwa! Ga mu hwa!!


(Ɗanƙwairo, Waƙar Musa Ɗanqwairo ta 'Ƴan doton Tsahe Aliyu & Gusau, 2003: sh. xi)


Domin haka, Musa Ɗanƙwairo ya na ƙullawa da rera ɗiya na waƙoƙinsa a yayin sadarwa.


Tawagar Ɗanƙwairo da matsayi


Ƙungiyar Makaɗa Musa Ɗanqwairo Maradun ta Kiɗan Kotso ta haɗa da:


i) Alhaji Musa Ɗanqwairo Maradun = Jagora


ii) Muhammadu, Daudun Kiɗa na Farko, Ya rasu = Kiɗa da Amshi


iii) Garba, Zwacin Kiɗa, Marafan Kiɗa,


Daudun Kiɗa na Biyu (2), Ya rasu = Kiɗa da Amshi


iv) Audu, Wakilin Kiɗa = Kixa da Amshi


v) Ali, Sabon Kiɗa (ɗan Sa'idu Shayi, Wani Ƙanin Musa Ɗanƙwairo) = Kiɗa da Amshi


vi) Sani, Zaƙin Murya, Marafan Kiɗa, Ya rasu = Kiɗa da Amshi


vii) Abubakar (Garba), Ciroman Kiɗa (ɗa), Ya rasu = Kiɗa da Amshi


viii) Ibrahim Sarkin Fada (Ɗane) = Kiɗa da Amshi


ix) Muhammadu Jikka (Jikka, Halifa 3) = Kiɗa da Amshi


x) Sani (Jika) = Kiɗa da Amshi


xi) Muhammadu Gambo (Bara) = Kiɗa da Amshi


xii) Malam (Bara) = Sanƙira, Kwandon Ɗanƙwairo


xiii) Ƙanƙahu (Bara) = Tsaron Kaya


xiv) Sada (Bara) = Sanƙira


xv) Rabo (Bara) = Kiɗa da Amshi


xvi) Nabuba (Bara) = Kiɗa da Amshi


xvii) Bucaca 'Yarkohji (Bara) = Kiɗa da Amshi


xviii) Amadu Bakura (Bara) = Sanƙira


xix) Sallah Kwana (Bara) = Hadimin Gidan Ɗanƙwairo


xx) Daudu Ɗangaladima (Bara) = Kula da Doki da Gona


Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa

Kamar yadda tarihin rayuwar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya tabbatar, shi mutum ne mai kula da ciyarwa da shayarwa da tufasarwa da samar da muhallai na zaman iyalinsa da makusantansu da sauran waɗanda suke majiɓinta a gare shi.


Sannan yakan yi wa iyalinsa tarbiyya gwargwadon yadda addinin Musulunci da al'adu kyawawa na Hausawa suka tanada.


Mutum ne kuma wanda yake fafutukar haɗa kan dukkan zuriyyarsa da yi musu addu'a su zauna salim alim ba ƙyama ko faɗa ba wata hauraƙiya ko ƙiyayyar juna. Haƙiƙa, wannan wata hanya ce ta wanzar da zuriyya bisa haƙuri don ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.


Musa Ɗanƙwairo kamar yadda ya tashi, ya gani a gidansu, ya himmatu ta fuskar yin noma da duka ayyuka na gona don samar da abinci da abubuwan masarufi waɗanda suka zamanto abokan zama.


Sau da yawa, Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ba ya buƙatar duk wani abu da zai hana shi yin noma a kowace faɗuwar damina. Ta haka Alhaji Musa Ɗanqwairo Maradun ya nuna ba ya son jama'arsa ta tagayyara.


Rasuwar Makaɗa Ɗanƙwairo, Sarkin Kiɗan Maradun

Sarkin Kiɗan Maradun, Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, bayan wata gajeruwar rashin lafiya, Allahu cikin ikonsa ya karɓi rayuwarsa a ranar Juma'a 13 ga watan Satumba, 1991.


Ya rasu a gidansa a Gidan Kano, Ƙaramar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara.


Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo

Bayanan hoto,

Tawagar Alhaji Danjuma Ɗanƙwairo na yanzu


Kalmar halifa a fage ko harka ta kiɗa da waƙar wani tasiri ne da wani ko wasu makaɗa suke yi har suke samu su dinga kwaikwayar ko su dinga yin biyayya bisa turba ta wani makaɗi, musamman wanda ya jima a aiwatarwa da sadar da waƙoƙin baka.


Sannan yin tasirin da wani makaɗi yakan zama biyayya ta fasalin kiɗa da waƙa ko yin ɗani na raujinsa ko ɗani na yanayin rerawarsa da sadar da waƙoƙinsa ko ɗani na tsarin ƙulli da ƙari a waƙoƙinsa wato yanayin aiwatar da waƙoƙinsa a sahun ƙunƙiya ko kaɗaita ko dai wani ɗani na yanayin dabarunsa na gudanar da waƙa da makamantan waɗannan halaye.


Halifantaka ta makaɗi tana iya zama kamar yadda Ɗan masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule (tattaunawa da shi a shekarar 2009) yake gani tana iya zama ta magaji a raye wato magaji da rai, ko ba rai wato Magaji bayan mutuwa.


Haƙiƙanin rayuwa yaƙini ta nuna, halifofin Makaƙa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun suna iya zama magada daga cikin zuriyyar Ɗanƙwairo kai tsaye wato magada na jini ko kuma magadan Ɗanƙwairo daga wajen zuriyyarsa.


Magadan nan sukan yi koyi da matakan tafiyar rauji na Ɗanƙwairo ko ta hanyar aiwatarwa ko ta hanyar matakan rerawa da na sadarwa ko ta neman tabarukki ko na sauransu.


Halifofin Musa Ɗanƙwairo na Jini

Kamar yadda aka nuna a baya, Halifofin Makaɗa Musa Ɗanqwairo na jini su ne 'ya'yansa da jikokinsa da tattaɓa-kunnensa da sauran ƴan zuriyyarsa waɗanda suka gaje shi a aiwatarwa da sadar da waƙoƙin baka na Hausa.


Halifantaka wata al'ada ce wadda Hausawa suka samar da ita bisa wasu zanguna a rayuwar Hausawa inda Hausawa magidanta sukan bukaci ƴaƴansu ko jikokinsu ko masu biyowa baya a ƙasansu su gaje su a harkokin da suke aiwatarwa. Hausawa ne ma suke cewa, Gado alala ga raggo.


Ga alama wannan ne ma ya sa wasu manazarta suke ganin koma baya ne idan makaɗi ba shi da Magaji domin gidansa zai yi ƙasa har yau da gobe ta sa ya ruguje (Abdullahi Umar Kafin Hausa (2002) sh. 241-255).


Babu shakka, tun Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo yana da rai ya fahimci zai bar zuriyya wadda za ta gaje shi a kiɗa da waƙoƙi na kotso kuma wadda ta gwangwaje a harka ta kiɗa da waƙa, kamar shi Musa Ɗanqwairo yadda ya gada daga wajen iyayensa da yayyensa da kakanninsa.


Halifar Ɗanƙwairo na farko na bayan rasuwarsa a 1991, shi ne yake faɗi tun mahaifin, Musa Ɗanqwairo, yana a raye:


Jagora(Daudu): Batun kiɗi ko ba ku nan yi mukai,


: Kun Karantar da mu, mun yi ƙidan baƙi,


: Mui wasulla, mun yi ta yi,: Yanzu ilmi mukai tun da mun sauka,


: In hwa waƙa ce duk mun,


: san yadda za mu ƙulla ta,


: In an ce mutum mai tujara ne.


: Sai ya haihwi ɗa mai tujaran nan,


: In an ce mutum ga shi samna ne,


: Sai ya haihwa samna haƙiƙan ne,


: In Allah yau wa mutum ƙwazo,


: Ya bar haihuwa ɗa nai ya lalace,


: Tun da gado ne,


'Y/Amshi: Mun gani tun ga ɗiyan masara,


: Abu goye kowa da gemunai,


: Shirya kayan faɗa Maigida Tsahe,


: Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.


(Ɗanƙwairo, Waqar Shirya Kayan faɗa, ta Aliyu II,da Gusau, 2019: sh. 103-104)


Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya sami ƴaƴa da jikoki nasa waɗanda suka gaje shi daga 1991 zuwa yau 2021 kimanin guda uku. Su ne kamar haka:


i) Alhaji Garba Musa Ɗanƙwairo (Garban Ɗanƙwairo), Zwacin Kiɗa, Marafan Kiɗi, Daudun Kiɗi na 2, Halifar Ɗanƙwaiiro na ɗaya.


Garban Ɗanqwairo ya rasu a shekara ta 2009. Ɗa ne na Musa Ɗanƙwairo.


ii) Alhaji Abubakar Musa Ɗanƙwairo, Ciroman Kiɗi Halifan Musa Ɗanƙwairo na Biyu. Ya rasu a shekara ta 2010. Ɗa ne na Musa Ɗanƙwairo.


iii)Alhaji Muhammadu Ɗanjimma ɗan Muhammadu Ɗanmakaɗa Shi ne Halifan Makaɗa Musa Ɗanƙwairo na uku daga 2011.


Jika ne na Makaɗa Musa Ɗanƙwairo. Shi ne kuma Halifan Musa Ɗanƙwairo na yau.


Halifofin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Daga Waje


Akwai kuma wasu makaɗa waɗanda suka zama halifofin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo daga wajen zuriyyarsaa rukumi ma biyu.


Su waɗannan makaɗa ba su da wata alaƙa ta jini da Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, sai dai su ma makaɗa ne waɗanda suke aiwatarwa da rerawa da sadar da waƙoƙin baka na Hausa.


Har wa yau kuma ire-iren waɗannan makaɗa ko barantakar waƙa ba su yi a ƙarƙashin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ba.


Su dai waɗannan makaɗa ma'abota sauraron waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo ne, har suka kwaɗaitu a yin ɗani na waƙoƙinsa bisa rauji na waƙoƙin Ɗanqwairo da dabarun sadarwa da kuma neman tabarruki, musamman dangane da shuhurar Musa Ɗanƙwairo.


Wasu daga cikin waɗannan makaɗa kuma suna amfani da abin kiɗa na Kotso irin samfurin wanda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi kaɗawa.


Sannan kuma makaɗan sukan aiwatar da duka waƙoƙinsu da suke shiryawa ne a bisa matakai da dabaru na Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.


Wasu daga cikin waɗannan makaɗa sun ƙunshi:


Abdul Salisu Ɗanƙwairon Zazzau Kotso


Abdullahi Sani Ɗanbawa Ɗanqwairon Gwambe Kotso


Abubakar Ɗan'auta Ɗanƙwairon Tarauni Kotso


Abubakar Ɗan'auta Ɗanƙwairon Unguwa Uku Kotso


Adamu Usman Ɗanƙwairon Nadauri Kotso


Ado Gwaram Ɗanƙwairon Gwaram Kotso


Ahmadu Garba Ɗanƙwairon Aucanawa Kotso


Alhaji Barau Ƙaya Ɗanƙwairon Ƙaya Kotso


Alhaji Musa Keɓɓe Ɗanƙwairon Kuci Kotso


Alhaji Sani Marafa Xanqwairon Wanke Kotso


Alhaji Ɗan'abai Ɗanƙwairon Ƙwaranyo Kotso


Alhaji Ɗanjumma Ɗanƙwairon Koko Kotso


Alhaji Ɗanzaki Ɗanqwairon Ƙaya Kotso


Amadu Monkey Ɗanƙwairon Sarkin Katsina Kotso


Auwalu Iguda Ɗanƙwairon Ma'aiki Sitidiyo


Bala Maikotso Ɗanƙwairon Ɓagwai Kotso


Bello Zaƙin Murya Ɗanqwairon Minna Kotso


Dadda'u Maikotso Ɗanƙwairon Katsina Kotso


Ɗan'imamu Ɗanƙwairon Sokoto Kotso


Ɗanjos Ɗanƙwairon Abuja Kotso


Ɗanladi Ɗanƙwairon Kaduna Kotso


Haruna Aliyu Ningi Ɗanƙwairon Ningi Sitidiyo


Haruna Idris Ɗanƙwairon Maƙarfi Kotso


Haruna Ɗanƙwairon Maƙarfi Kotso


Imam Sanusi Imamu Ɗanƙwairon Katsina Kotso


Kabiru Arafa Ɗanƙwairon Dawakin Kudu Kotso


Lawali Jibiya Ɗanƙwairon Jibiya Kotso


Muhammad Sani Ɗanƙwairon Funtua Kotso


Muhammadu Mande Ɗanƙwairon Katagum, Azare Kotso


Muhammadu Musa Ɗanƙwairon Sarkin Kazaure Kotso


Muhammadu Ɗandare Ɗanƙwairon Jere Kotso


Musa Kuɗahi Fakku Ɗanƙwairon Fakku Kotso


Musa Santolo Ɗanƙwairon Zangon Daura Kotso


Mustafa Marafa Ɗanƙwairon Dole Zamfara Kotso


Mustafa Umar Ɗanƙwairon Kurna Kotso


Sa'adu Umar Ɗanƙwairon Yobe Kotso


Sabi'u Lawal Gargai Xanqwairon Dade Kotso


Salisu Inuwa Ɗanƙwairon Kano Kotso


Shehu Adamu Ɗanƙwairon Zigau Kotso


Shehu Inuwa Maikotso Ɗanƙwairon Kano Kotso


Shehu Inuwa Ɗanƙwairon Kumbotso Kotso


Shehu Sani Ɗanƙwairon Randale Kotso


Sunusi Bello Ɗanƙwairon Gwarzo Kotso


Umar Idris Ɗanƙwairon Biu Kotso, Jita


Umar Idris Ɗanƙwairon Biu Sitidiyo


Umaru Bakari Ɗanƙwairon Taraba Kotso


Usaini Ciroma Ɗanƙwairon Kano Kotso


Yusuf Ɗanƙwairon Yawuri Kotso


Yusuf Almisiriyya Ɗanƙwairon Annabi Sitidiyo


Yusuf Ɗahiru Ɗanƙwairon Ma'aiki Sitidiyo


Yusuf Ɗanƙwairon Bargu Kotso


Rahotun BBC


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN