Yan fashi sun kwace kudi da mota yayin da wani Hedimasta ke tsakar yin lalata da masoyiyarsa a cikin motar


Shugaban makarantar Sakandare na David Livingstone High School da ke garin Ntabazinduna a kasar Zimbabwe ya rasa motarsa kirar Ford Ranger mai darajar kudin Amurka Dala US$50,000 bayan Yan fashin da makami guda biyu sun kwace motar da kudin.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa Hedimastan mai suna Vusumuzi Nkiwane ya rasa motar da kudin ne lokacin da yake tsakar yin lalata tare da budurwarsa a cikin motar ko da Yan fashin suka farmake shi.

Safeton yansanda Abednico Ncube ya ce lamarin ya faru ne a kusa da dajin United College of Education. Ya ce Hedimastan yana tsakar holewa da budurwarsa a cikin motar mallakin makarantar da yake aiki, kwatsam sai wasu Yan fashi guda biyu suka bullo rike da Adda da wuka, kuma suka bukaci ya basu kudi da kuma makullan motar.

Ya ce da farko Hedimastan ya ki ya basu kudin da makullan motar. Sai dai ala tilas ya basu abin da suke bukata bayan sun caka masa wuka a cinyarsa.

Daga bisani Yan fashin sun tilasta Hedimastan da masoyiyarsa suka fita daga cikin motar sai Yan fashin suka shiga suka gudu da motar da kudin da ke cikinta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN