Yadda sojoji suka yi wa direban tasi dukan fitar rai a Jos


Sojojin da ke aiki da Operation Safe Haven (OPSH), wata hukumar tsaron hadin guiwa da ke da alhakin samar da zaman lafiya a Plateau, a daren Juma'a, ana zarginsu da yi wa direban tasi mai suna Sadik Abdullahi Karafa dukan mutuwa.

Daily Trust ta ruwaito yadda ake zargin sojojin da yi masa dukan a kasuwar Paringada yayin da ya ke hanyar dawowa daga Mangu, sa'a daya kafin dokar ta bacin ta fara aiki

Dokar ta bacin ta na aiki ne daga karfe goma na dare zuwa shida na safe amma Sadik ya dawo wurin karfe tara da minti ashirin na dare, Daily Trust ta wallafa.

Abdullahi Karafa, wani babban yayan mamacin, ya bayyana cewa sojoji ne suka halaka kaninsa.

Ya ce:

"Mu na gida lokacin da wani abokinmu ya kira ni kan cewa sojoji sun kama kanina kuma suna dukan shi a wurin babban titin Faringada. Da jin haka, daya daga cikin kannanmu, Umar Abdullahi ya hanzarta zuwa wurin kuma ya samu sojojin suna dukan shi.

"Lokacin da ya sanar da su cewa Sadik dan uwan shi ne, sun yi banza da shi tare da saka shi a Hilux. Kaninmu ya dawo gida daren Juma'a kuma mun yanke hukuncin zuwa da safe. Da safiyar Asabar mu ka je Faringada inda muka tarar da gawar shi.

“Mun dauka gawar shi inda muka kai ta ofishin 'yan sandan Katako domin kai rahoton lamarin. Ba bu wani bayanin dalilin da yasa aka mishi mugun dukan. Kwamandan Div 3 ya kawo mana ziyara tare da alkawarin cewa za a tabbatar da an yi adalci. Ba za mu bar wannan abun ba, muna neman adalci," ya kara da cewa.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun OPSH, Ishaku Takwa, ya ce zai bincika kuma zai kira mu, amma har yanzu shiru.

Legit Nigerian

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN