Miyetti Allah ta ce farashin saniya zai koma N2m idan aka hana kiwo a fili


Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana cewa farashin saniya na iya kai wa sama da naira miliyan biyu a jihar Legas idan aka amince da rattaba hannu kan dokar hana kiwo a jihar.

Sakataren shiyyar Miyetti Allah a Kudu maso Yamma ne ya bayyana haka, yayin zaman sauraron ra'ayoyi na kwana daya da majalisar dokokin jihar ta shirya kan dokar hana kiwo a ranar Laraba 8 ga watan Satumba.

A yayin taron, Usman ya roki gwamnatin jihar da ta taimakawa makiyaya, lura da cewa kiwon dabbobi ya fi tsada idan aka yi shi a kebe.

Usman, wanda ya amince da cewa akwai wasu makiyaya masu aikata laifuka, ya bayar da hujjar cewa kiwon saniya a wuri guda na iya kara farashin saniya zuwa Naira miliyan biyu.

Ya kuma roki gwamnati da ta bada tallafin kudin kiwon shanu a wuri daya.

A kalamansa:

“Idan ana kiwon shanu a wuri daya, farashin zai iya kaiwa kusan Naira miliyan biyu kowanne. Mun amince da wasu hakimai a wasu jihohi cewa duk wanda ke son kiwon shanu a wani wuri to ya yi rajista kuma ya fadi lokacin da zai tafi."

Hakanan, Shugaban Kungiyar Mahauta ta Jihar Legas, Alhaji Alabi Bamidele Kazeem, ya ba da shawarar tallafi ga makiyaya shanu, yana mai cewa “kiwon dabbobi a wuri daya yana da tsada”.

A nasshi bangaren, Shugaban kungiyar makiyaya tumaki na jihar Legas, Alhaji Mustapha Ibrahim, ya bayyana kudirin a matsayin “wanda zai hada kan kowa da kowa kuma zai tabbatar da alakar da ke tsakanin masu kiwo da manoma”.

A ba mu lokaci mu horar da Fulani makiyaya, Miyetti Allah ta roki Legas

A bangare guda, kungiyar ta ce tana bukatar lokaci don horar da membobinta kan yadda za a daina yawon kiwo a fili, TheCable ta ruwaito.

Usman ya ce membobin kungiyar suna bukatar lokaci don a karantar da su kan “yadda za su yi kiwo a wuri daya kuma ba za su taka kasar kowa ba”.

A cewarsa:

“Makiyayanmu ba su saba da kiwon shanu wuri daya ba. Suna tafiya ne daga nan zuwa wani wuri. Idan muka ce za mu ajiye shanu wuri daya, mai shanun ba zai sami kudin ciyar da dabbobin a wuri daya ba.

Sun riga sun dogara da tafiya daga wannan wuri zuwa wani. Domin a lokacin damina, muna da inda muke sauka, kuma muna da inda muke sauka a rani.

“Muna rokon gwamnatin jihar Legas da ta ba mu lokaci mu je mu fada wa mutanenmu kuma mu horar da su yadda za su yi kiwo a wuri daya kuma kada su fada zuwa kasar kowa.

"Amma kiwo a wuri daya, a yanzu, mutanen mu ba su da ikon yin hakan. Abin da ba ku saba da shi ba, dole ne a koyar da ku. Kuma a hankali, kowa zai fahimta.”

Legit Nigeria

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN