Da duminsa: Matsafi ya kashe karuwa ya gundule kanta ya gudu da shi, yansanda na nemansa ruwa a jallo


Rundunar yansandan jihar Kwara ta kama mutane biyar bisa zargin kashe wata karuwa suka sare kanta domin dalilan tsafi a karamar hukumar Patigi.

Kakakin hukumar yansandan jihar Okasanmi Ajayi, ya sanar wa manema labarai ranar Juma'a 10 ga watan Satumba. Ya ce wadanda aka kama sun hada da Samuel Peter Tsado, Mohammed Gbara a.k.a. Madi, Abubakar Mohammed a.k.a. Mallam Baba Pati, Mohammed Ahmadu Nma da Bala Karin. Sai dai mutum uku cikin wadanda ke da hannu a lamarin sun tsere.

Ya ce, Samuel Peter Tsado ne ya je wani Otel ya yi hayan wata karuwa domin kwanan gida a kan N5000, sai dai bayan sun isa gidanshi da karuwar ne, sai abokinsa wanda yake labe a cikin dakin ya fito suka shaketa ta mutu sai suka yanke kanta da wuka.

Kakakin ya ce daga nan ne suka watse daga bisani suka sake haduwa a jihar Niger, yayin da suke jiran isowar matsafin da zai yi masu kudi da kan karuwar.

Asirinsu ya tonu ne bayan an sanar da yansanda cewa ba a gan karuwar ba na tsawon kwanaki. Sakamakon haka yansanda suka shiga bincike da ya yi sanadin kama wadannan mutane. An gano gawar karuwar a wajen da suka jefar da ita a cikin jeji. 

Yansanda na kokarin nema tare da kama wanda ya tafi da kan karuwar a cikin matsafan tare da kama sauran mutum uku da suka tsere.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari