Abin da ya sa muke so a rage yawan Masallatai a Kano'- Majalisar Malamai


Majalisar Malamai ta ƙasa reshen jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilanta na yin kira a rage gina Masallatai barkatai a jihar.

A wata sanarwa da ta fitar bayan wani babban taron da ta gudanar na kwana biyu a ƙarshen makon da ya gabata a Kano, majalisar ta bayyana jerin sharwari da manufofin da ta cimma a wajen taron, kuma ciki har da rage yawan buɗe masallatai.

"A rage buɗe masallatai barkatai domin guje wa rarraba kai da zukatan al'umma," a cewar sanarwar da majalisar malaman ta fitar bayan kammala taron,

Amma cikin sanarwar, an yi kira ga malamai da limamai su dinga raya masallatai da karatuttuka da lakcoci baya ga tsayar da sallah a cikinsu.

Taron na haɗin gwiwa da Sashen Nazarin Addinin Musulunci da Shari'a na Jami'ar Bayero, ya ƙunshi wakilai na malamai da limamai na ƙananan hukumomin jihar Kano 44 da shugaban Jami'ar Bayero da wakilcin Kwamishinan Lamuran Addini Dr Muhammad Tahar Adamu.

Majalisar Malaman ta ce taronta ya mayar da hankali ne kan gudunmawar malamai da limamai wajen samar da tarbiya da inganta zaman lafiya da dora al'amura bisa tushen shari'ar Musulunci.

Kuma an gabatar da maƙaloli tare da yin ta'aliki kan makalolin da aka gabatar. Daga cikin matsayar da taron ya cimma, majalisar malaman ta ce "yin haka zai inganta zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya."

Sanarwar ta ƙara da cewa mahalarta taron sun yi takaicin yadda wasu malamai suke zubar da dajararsu ta hanyar yadda "suke bin ƴan siyasa suna masu yin biyayya."

Haka kuma malaman na Kano sun ce akwai wasu bara-gurbin malamai da ke haddasa rikici da rarrabuwar kai a cikin majalisar malamai domin cimma burinsu na kashin kansu.

'A riƙa yi wa masu mulki nasiha'

Majalaisar malaman ta ce malamai da limamai sun bayar da gudunmawa mai yawa a tarihin musulunci wajen jagorantar al'umma game da tarbiyya da shugabanci na gari da zaman lafiya da samar da tsaro

"Wannan ya sumu ne ta hanyar kyawawan dabi'u da taƙawa da tawali'u da gaskiya da magabata a cikin malamai da limamai da suka siffatu da ɗora al'umma kan biyayya da shugabanci da ilimi."

Amma majalisar ta ja hankalin mambobinta kan haƙƙin da ke kansu na yi wa masu mulki nasiha.

Ta yi kira ga malaman cewa: "A riƙa yi wa masu mulki a kowane mataki nasiha kan nauyin da ke kansu."

Ta kuma yi kira da a zaburar da matasa da majalisar ta ce - masu tarbiya game da shiga ayyukan tsaro da harkokin siyasa da shugabanci.

Majalisar ta kuma buƙaci malamai da limamai su rika girmamawa da ziyartar junansu domin samar da hadin kai da fahimtar juna domin zaman lafiyar dalibai da sauran al'umma.

Majalisar ta kuma jaddada cewa tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka da aka yi mata rijista, don haka ta ja hankalin mambobinta cewa "babu wanda zai yi mata karfa-karfa ya sa ta yi abin da ya saɓa wa doka da ka'idoji da sharuɗɗanta."

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE