6, Budurwa Saurayina da muka yi shekaru 4 tare ya yi wuf da ƙawata da suka haɗu cikin watanni 6, Budurwa


Cikin takaici da cizon yatsa wata budurwa ta garzaya dandalin sada zumunta na zamani inda ta bayyana yadda saurayin ta ya yaudare ta, rahoton LIB.

A cewar ta ya yanke shawarar auren wata daban wacce ya hadu da ita ta wurin budurwar sa cikin watanni 6 kamar yadda LIB ta ruwaito

Budurwar ta ce sun kwashe shekaru hudu su na kwasar soyayya ashe duk yaudarar ta yake shirin yi.

Budurwar, wacce ‘yar kasar Afrika ta Kudu ce ta bayyana yadda duk da sun kwashe shekaru 4 kwatsam ya juya mata baya.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta:

“Saurayi na wanda muka kwashe shekaru 4 muna soyayya zai auri wata da ya hadu da ita ta hanya ta cikin watanni shida.”

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyin su game da lamarin, wasu suna ganin saurayin ba shi da laifi yayin da wasu kuma suke ganin ya ci amana.

Legit Hausa


Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari