Rundunar yansandan jihar Ogun ta kama wata mahaifiya mai suna Kafayat Lawal yar shekara 45 bisa zargin yi wa diyarta yar shekara 17 mai suna Ayomide Adekoya duka har ta mutu.
Kakakin hukumar yansandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce mahaifiyar yarinyar ta yi kokarin yi wa yaranta biyu yan mata Blessing Adekoya mai shekara 19 da kanwarta Ayomide Adekoya mai shekara 17 duka saboda sun fita yawo basu dawo ba sai washegari.
Sai dai makwabta sun shiga tsakani suka roke ta kuma aka ja wa yaran kunne. Ya ce bayan kwana biyu sai yaran su biyu suka sake fita suka je yawo basu dawo ba sai washegari.
Sakamakon haka mahaifiyarsu ta fusata ta saka su a cikin daki ta kulle su ta yi masu dukan fitan albarka, kuma ta yi wa Blessing rauni da fasashshen kwalba a hannu, kuma ta caka wa Ayomide fasashshen kwalbar a kirji.
An garzaya zuwa asibiti da yaran bayan samun raunukan, sai dai Ayomide ta mutu lokacin da take karbar magani a Asibiti. Sakamakon haka yansanda suka kama mahaifiyarsu kuma ana gudanar da bincike.