Tuna baya "Ba abinda ke cin dan Siyasa da wuri kamar yin karya" - Hon. Yakubu Rilisco


A ranar Asabar 15/7/2017,  shafin isyaku.com ya tattauna da Hon Muhammad Bello Yakubu Rilisco a wancan lokaci dan Majalisar dokoki na jihar Kebbi ne, kan mahanga ta siyasa da alkiblar da siyasar jihar Kebbi ke fuskanta.

Ga martanin Hon Rilisco


A yau shafin labarai na ISYAKU.COM ya tuntubi dan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi Hon.Bar Muhammed Bello Yakubu Rilisco akan ko yaya yake ganin Siyasa da yadda ya kamata a tafiyar da tsarin Siyasa a jihar Kebbi?

"Hon Rilisco ya ce da farko dai Siyasa ba fitina bane, ra'ayi ne kuma kowa zai iya yin abinda yaso ta hanyar zaben wanda yake so. Yadda kake da naka ra'ayi haka wani yana da nashi ra'ayi. Saboda haka mataki na farko shine a mutunta juna.

Yin zabe ta hanyar fitowa a kada kuri'a wata dama ce da mutum ke da ita domin rashin fitowa a yi zabe ya zama cutar da kai da kuma cutar da al'umma.  Don rashin kada kuri'ar ka zai iya sa wanda bai cancanta ya ci zabe ba yazo yaci zaben kuma daga baya jama'a su dinga kuka akai.


Wadanda aka zaba kuma su sani ba wai mutum an zabe shi ne yazo yayi iko ba, yazo ne yayi wa mutane aiki. Ya kamata ya dauki kanshi kamar shine bawan jama'a,  ba wai maigidan jama'a ba. Saboda su ne suka taru suka jefa maka kuri'a ka kai kan kujera da matsayin da kake.

Haka ya isa ka sani cewa ba za ka iya kaiwa kan matsayi, ko kujerar da kake ba sai jama'a sun kaika ta hanyar zabe. Idan ka kai kan kujerar sai ka kalli mutane da mutunci,  da idon rahama, Abin da zai yiwu da gaske kayi masu, 

Idan jama'a sunzo wajen ka,  ka saurare su. Abinda za ka iya yi ka yi ,kada kayi karya. Domin ba abinda ke cin dan Siyasa da wuri kamar yin karya, ko yin alkawarin karya. Saboda haka ka bi gaskiyar ka, wannan itace maganar gaskiya."

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari