Cikin hotuna: Yadda girgizan kasa ya yi sanadin mutuwar mutum 230 a kasar Haiti, duba yadda ta faru


An yi girgizan kasa mai karfin 7.2 a yammacin kasar Hiti ranar 14 ga watan Agusta, lamari da ya yi sanadin mutuwar mutum 230 tare da haddasa barna mai yawa ga gidaje da dukiyan jama'a. Shafin labarai isyaku.com ya ruwaito.

Girgizan kasar daya auku da karfe 8:29 agogon yamma maso gabas na kasar, ya haifar da tunanin yadda girgizan kasa ya afka wa yankin Caribbean a shekara 2010 lamari da ya haifar da mutuwar fiye da mutum 200.000. Sakamakon haka Firaministan kasar, Ariel Henry ya sa dokar ta baci na wata daya.

Wani jami'in ma'aikatar kula da fararen hula na kasar Haiti Jerry Chandler, ya ce adadin wadanda suka mutu ya karu daga 29 zuwa 227. ya ce za a tura ma'aikatan ceto da agaji domin zakulo wadanda ke bukatar taimakon gaggawa.

Sashen hasashe da kula da yanayi na kasar Amurka, ya ce fadin girgizan kasar ya kai mil 78 daga yammacin babban birnin kasar Port-au-Prince.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari