An sanya dokar hana fita a wasu yankunan jihar Filato bayan kisan mutum 30 Musulmai matafiya


Gwamnatin Jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta ƙaƙaba dokar hana fita a ƙananan hukumomi uku daga ƙarfe shida na yamma zuwa ƙarfe shida na safe. BBC Hausa ta ruwaito.

Kananan hukumomin sun haɗa da Jos Ta Kudu da Jos ta Arewa da kuma Bassa.

An dauki matakin ne bayan wasu sun kashe aƙalla mutum 30 matafiya tare da jikkata wasu da dama a Jos babban birnin Jihar ranar Asabar.

Kwamishinan Watsa Labaran jihar, Dan Majang, ya faɗa wa BBC cewa sanya dokar hana fitar na da nasaba da kisan "matafiya musulmi 23 da ke kan hanyar su ta komawa kudancin Najeriyar daga jihar Bauchi."

Sai dai wasu bayanai na cewa adadin mamatan ya fi haka, kuma akwai da dama da suka tarwatse da har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

A cewar Dan Manjang "matafiyan ƴan asalin jihar Ondo ne da suka fito daga jihar Bauchi bayan halartar wani taro sai wannan hargitsi ya rutsa da su."

Wasu rahotanni sun ce matafiyan sun halarci bikin sabuwar shekarar musulunci ne a garin Bauchi da ke maƙwabtaka da garin Jos na jihar Filato.

Kan ko sun san ko su waye su ka yi wannan ta'asa, Kwamishinan ya ce "ya yi wuri mu iya tantance ko su waye. Amma yanzu haka an kama kusan mutun 20 da ake zargi kuma yan sanda na kan yi musu tambayoyi."

Ya kuma tabbatar da mutuwar mutum 23 inda ya ce wasu ƙarin 23 suna kwance a asibiti.

Sai dai wani ɗan jarida da ya ziyarci asibitin yankin ya faɗa wa BBC cewa ya ga gawar mutum 30, yayin da wasu ke jinya.

Akasarin mutanen na ɗauke da sara na adduna da sauran makamai a jikinsu.

Ya zuwa yanzu babu tabbacin abin da ya haddasa rikicin, amma lamarin ya faru ne 'yan kwanaki bayan wani tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu manoma 'yan ƙabilar Iregwe.

Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, Gwamna Simon Bako Lalong ya yi tur da harin sannan ya gargaɗi "masu tayar da fitina da su guji yin hakan" saboda "gwamnati ba za ta lamunci tayar da hankali ba".

Da ma dai an shafe shkara da shekaru ana fama da rikicin kabilanci a jihar ta Filato, amma tun hawan Gwamna Lalong kan mulki lamuran tsaro sun inganta.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN