Rundunar yansandan jihar Kano ta kama tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Wannan ya zo ne awanni kadan bayan Majalisar Dokokin jihar Kano ta bayar da shawarar kamawa tare da binciken tsohon shugaban hukumar.
Daily trust ta ruwaito cewa yansanda sun gayyace shi ne domin ya amsa tambayoyi kan zargin rahotun Likita na bogi.
Kazalika yansanda na bincikensa kan takardar bogi da ya shafi Majalisar Dokokin jihar da wata takardar bogi da ake zargi daga ofishin Akanta janar na jihar Kano.
Kakakin hukumar yansandan jihar Kano DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da cewa Rimin Gado na amsa tambayoyi daga masu bincike.
Ya ce ana binciken Rimin Gado kan zargin bayar da bayanin karya da bayar da takardar bogi.