Za ka iya amfani da Shafin labarai na isyaku.com domin tallata kasuwancinka domin more wa tsarin zamani wajen isar da sakonka ga jama'a.
Akwai adadin maziyarta miliyan shida da dubu dari shida da sittin da bakwai da dari bakwai da kari, kuma adadin maziyarta shafin na karuwa a kullum. Za ka iya ganin haka a ma"aunin adadi da ke kasan shafin isyaku.com.
Shafin labarai na isyaku.com yana cikin group na WhatsApp guda dari uku da daya 301 bayan group na kampanin isyaku.com guda goma sha takwas 18, kuma adadin na ci gaba da karuwa.
Shafin labarai na isyaku.com na gudanar da ayyukansa ne a ƙarƙashin kampanin Seniora int'l Ltd RC 1470216. Wanda ke da damar gudanar da kasuwanci ta bangarori da dama, wasu daga ciki har da:
1. Tattara bayanai don amfanin al'umma.
2. Gudanar da binciken kwakwaf wajen aikin labarai da samar da labarai.
3. Tallata sanaoi ta yanar gizo da duk wata hanya ta zamani.
4. Shirya finafinai, wakoki domin kasuwaci, sayarwa, dillaci ko wallafawa.
5. Shirya gasa ko bayar da lambar girma ga zakaru a fannonin bajinta.
6. Tsarawa tare da kirkiro dubarun isar da sako ga jama'a a fasahance.
Da dai sauran ababen da hukumar CAC ta bamu izinin gudanarwa.
Ababen da za mu yi maka
1. Za mu isar da tallarka ga jama'a a fiye da group 320 na WhatsApp.
2. Za mu isar da sakonka ta yanar gizo ga duk mai shiga yanar gizo domin neman bayani.
3. Za mu haskaka kasuwancinka kamar farin wata cikin duhun dare.
4. Duniya za ta san da kasuwancinka cikin lokaci kalilan.
Ku tuntube mu a 08062543120 ko a ofishin mu da ke lamba 50 Taushi Plaza, Akmadu Bello way Birnin kebbi, jihar Kebbi.