Tagwayen yan matan nan guda biyu yan shekara 16 da wani yaro ya yi masu cikin shege a kasar Cameroon sun haihu.
Tagwayen sun haifi yaya maza kowacensu kuma sun haihu lafiya kalau, jarirai da suka haifa suna cikin koshin lafiya.
Wata makusanciyar tagwayen mai suna Ayisha Togina ta sanar da zancen ranar Juma'a 23, bayan ta dade tana biye da lamarin tun farkonsa.
Kazalika Ayisha tare da abokanta sun samar wa tagwayen daki daya, suka gyara masu domin gudanar da rayuwa tare da jarirai da suka haifa.