Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed, ya ɓalle daga jam'iyyar APC ta jihar Kwara, ya bude sabuwar Sakatariya


Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ɓalle daga jam'iyyar APC ta jihar Kwara, inda ya bayyana cewa bada jimawa ba za'a canza rijistar yan jam'iyya a jihar, kamar yadda punch ta ruwaito.

Muhammed, wanda yayi jawabi a wurin buɗe sabuwar sakateriyar APC ta ɓangarensa a Ilorin, ranar Asabar, yace rijistar yan jam'iyyar da aka gudanar a jihar ba mai inganci bace.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar da kuma ɓangaren ministan yaɗa labaru sun gudanar da ganganmi daban-daban na murnar cikar APC shekara biyu a kan mulki.

Yayin da ɓangaren gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman Abdulrazaq, yake da sakateriyar jam'iyya a yankin Tanke, ɓangaren minista Lai ya ƙaddamar da tasa sakateriyan a GRA, Ilorin.

Muhammed, yace: "An sanya son rai a rijistar zama ɗan jam'iyya da aka gudanar ba da jimawa ba saboda mafi yawancin mambobin APC ba su samu damar yin rijista ba."

"Lokacin da muka gano haka, da ni da tsofaffin yan takarar gwamna biyu, Prof Oba AbdulRaheem da Alhaji Tajudeen Audu, sai muka garzaya wurin uwar jam'iyya ta ƙasa."

"Mun je mun faɗawa shugaban kwamitin riƙo, Mai Mala Buni, kuma ya tabbatar mana da cewa za'a sake gudanar da rijista a jihar."

Gwaman Kwara ya zargi manyan APC da karkatar da kuɗi

A ranar 26 ga watan Yuni, Gwamna AbdulRazaq, ya zargi jiga-jigan APC na jihar cewa sun karɓi maƙudan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe a 2019, amma ko sisi ba su kawo masa ba.

Amma Lai Muhammed ya fito ya musanta wannan zargin, ya bayyana cewa babu wani gwamna ko minista da ya bashi sisin kobo tallafin yaƙin neman zaɓe a 2019.

"Ban karkatar ko naira ba daga cikin kuɗin yaƙin neman zaɓen APC a 2019 kamar yadda Gwamna AbdulRazaq ya yi zargi," Lai ya faɗa.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari