Labarin Fulani makiyaya masu askin ciko da sha'awar mawakan hiphop


Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa sanya dan kunne da gyara gira da yin askin ciko ba abubuwa ba ne da ake sa ran Fulani makiyaya a Najeriya za su yi
, saboda suna kwashe galibin rayuwarsu ne a cikin daji suna kiwon dabbobi.

Amma a lokutan bukukuwa, kamar bikin Sallah karama ko Babba, idan suka shiga cikin birane a arewacin Najeriya da ma babban birnin kasar, suna yin shiga irin ta 'yan gayu.

Kuma ba kamar sauran Musulmai da ke sa tufafi na gargajiya ba, wadannan Fulani makiyaya suna sanya tufafin turawa irin na mawakan hip-hop.

Fulani men in colourful outfits

Suna sanya rigunan jackets, da manyan takalma da rigunan sanyi irin wadanda mawakan Amurka a shekarun 1990 suke sanyawa, yayin da da dama daga cikinsu suke sha'awar wakokin turawa.

Sun sha cewa suna sha'awar Naira Marley, mawakin nan da ke Lagos, inda suke kwaikwayon askinsa da salon rayuwarsa, duk da yake suna zaune a yankunan Abuja, babban birnin kasar.

"Ina son Marley," a cewar Musa Sani, wanda yake rataye da rediyon da aka sanya wa MP3 da ke fitar da sautin kida kuma ana iya ganin wandonsa ya sauko kasa kadan daga kugunsa a wani salo irin na 'yan gayu.

A Fulani boy with a punk hairdo and radio across his chest
1px transparent line

Shi da wasu Fualnin kusan 300 sun taru a wani fili da ke yankin Lugbe a wajen birnin Abuja kusa da filin jirgi, saboda hukumomi sun rufe wuraren shakatawa domin hana yaduwar cutar korona.

A filin, wanda suke shan hantsi sannan babu jami'an tsaro, matasan Fualni makiyayan sun samu isasshen lokacin da za su sha iska su dauki hotuna ta hanyar amfani da wayoyinsu na salula.

Fulani man holding out his chain
1px transparent line

A yayin da matasan suke cikin gari tare da abokansu domin kashe kwarkwatar idanunsu da gudanar da bukukuwan sallah, su kuwa manyansu suna can gida suna gudanar da taruka na Ardo-Ardo.

Ana ganin rashin kunya ne idan matasan Fulani makiyaya suka halarci taron da manya suke yi, don haka haka manyan suke yin mazansu a gida yayin da matasan suke shiga birnin Abuja domin shakatawa.

A Fulani boy with a punk hairdo
1px transparent line

'Yan Najeriya kalilan ne, musamman wadanda ke zaune a kudancin kasar, suke ganin Fulani makiyaya suna yin shiga irin ta mawakan turai.

Galibin mutane suna ganin Fulani makiyaya ne tare da dabbobinsu suna kiwo, lamarin da a wasu lokuta yake janyo takaddama tsakaninsu da manoma har ta kai ga rasa rayuka.

Fulani makiyaya maza ne suka fi yin kiwo. Akasari ana ganinsu sanye da 'yar-shara da malafa da kuma takalman roba.

A Fulani herder with his cattle

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

A Fulani herder with his cattle

ASALIN HOTON,AFP

Don haka idan aka ga sun yi shiga irin ta mawakan turai sukan ja hankalin jama'a.

Suna sanya tabarau masu kyawu da wandunan jeans da suka yage da kananan riguna na shirts abin da ke sa su fito a wani salo mai ban sha'awa.

Fulani men in colourful outfits
1px transparent line
A smiling girl being hugged from behind
1px transparent line
A boy in colourful shirt
1px transparent line

Galibin maza a arewacin Najeriya suna sanya tufafi samfurin kaftani da aka dinak da yadi ko shadda.

Kazalika masu sukuni suna sanya babbar-riga.

Two Hausa teenagers in kaftan
1px transparent line

Su ma mata suna yin shiga mai kyawu ta atamfa sannan su yi kunshi.

A Fulani woman
1px transparent line
A Fulani woman
1px transparent line

Najeriya kasa ce mai riko da addini da al'ada, kuma kamar sauran kaliu, Fulani da Hausawa wadanda galibinsu Musulmai ne, suna bin al'ada sawu da kafa.

Sai dai duk da yake Fulani makiyaya suna kwaikwayon mawakan turai ta hanyar sanya tufafi irin nasu da ma sauraren wakokinsu, hakan ba "wani sabon abu ne", a cewar wani mai daukar hotuna Mudi Odibo, wanda ya shafe fiye da shekaru goma yana daukar hotunansu.

Two Fulani men in red and yellow clothes
1px transparent line

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN