Hayaƙin Janareto Ya Kashe Mutum Huɗu Ciki Har Mata Da Mijinta Yayin Bikin Sallah a Kwara


Wani abin bakin ciki ya faru a jihar Kwara, a ranar Laraba, a yayin da hayaki daga janareta ya yi sanadin rasuwar mutane hudu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a gidan Ojomu a Snmora, karamar hukumar Irepdun a jihar ta Kwara.

Wadanda abin ya faru da su sun taho daga Legas ne domin yin bikin sallah a Kwara.

An kai gawarwakinsu wurin ajiyar gawa a babban asibitin Offa.

Wasu mutane biyu da suka shaki hayakin janareton suna nan a asibiti ana basu kulawa bayan an gano su a sume.

Wata majiya ta ce DPO na Agbamu, Igbasan Owoyemi John, yana daga cikin wadanda suka zo kwashe gawarwakin.

A cewar majiyar:

"Mun gano gawaraki a safiyar yau, mai gida, matarshi da kawarta da abokin daya daga cikin yaran mai gidan da ya biyo su Legas domin bikin sallah.

"Wata dattijuwa da ke gidan ne ta gano gawarwakin a lokacin da ta tafi gaishe su da safe bayan karfe 7 a ranar Laraba.

"Biyu daga cikinsu da ke da rai an same su ne a sume da safen ranar Laraba. Sune kwance a asibiti rai hannun Allah kuma bamu san rannan da za a sallamo su ba."

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya kara da cewa:

"Eh, yanzu na kira jami'an mu da ke wurin. Da gaske ne abin. Za mu cigaba da kira ga mutane su rika kula da lafiyarsu a lokutan bukukuwa. Muna mika ta'aziyyar mu ga iyalan wadanda abin ya shafa."

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN