Gwamna Bagudu zai gina wani abu muhimmi mai tsawon kilomita 700 a kananan hukumomi 21 da ke jihar Kebbi


Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana aniyarta na shirin gina hanyoyin mota mai tsawon kilomita 700 a yankunan karkara a kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar. NAN ta ruwaito.

Kwamishinan ayyukan gona Alhaji Abdullahi Maigari, ya sanar da haka a garin Birnin kebbi ranar Talata, lokacin da Kawamishinan ma'aikatar watasa labarai na jihar Kebbi Hajiya Rukayya Tanko Ayuba ta jagoranci Yan Jarida a wata ziyara da suka kai ofishinsa.

Kwamishinan ya ce bayan sauwaka zirga zirgan kai kayakin gona zuwa garuruwa hakan zai taimaka wajen inganta aikin gona a fadin jihar Kebbi.

Ya ce shirye shirye da aka sa gaba zai habbaka dogaro da aikin gona da zai samar da tsarin saka jari a aikin gona lamari da zai samar da aikin dogaro da kai, kuma za a yi takama da shi a fadin Najeriya. 

Ya ce Gwamnatin jihar Kebbi tare da hadin gwiwa da OXFAM za ta samar da irin shuka daban daban har miliyan 1.3 da kuma iri na itatuwa daban daban a jihar Kebbi. 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN