Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Asabar 20 ga watan Yuli kasancewa ranar babbar Sallah, wanda ya yi daidai da ranar 1 ga watan Dhul-Hijja 1442AH.
Sanarwar haka ta fito ne daga Prof. Sambo Junaidu, babban hadimi kan harkar addini ga Majalisar Sarkin Musulmi ranar Lahadi.
Ya ce Mai Martaba Sarkin Musulmi ya yi na'am da rahotun da kwamitoci biyu na Masarautar, da na duban wata suka gabatar masa bayan ganin jinjirin watan Dhul-hijjah.