Cikakken rahotun Muƙabalar Abduljabbar da malaman Kano: Muhimman abubuwa 10 da suka faru a muhawarar


Bayan jiran watanni da aka yi, an gudanar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malamai a Jihar Kano ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021 wadda gwamnatin jihar ta shirya.

'Yan jarida ƙalilan ne suka shiga ɗakin muƙabalar ciki har da wakilin BBC Hausa a Kano Khalifa Shehu Dokaji. Jami'an tsaro sun yi wa ofishin Hukumar Shari'a ta Kano tsinke, wurin da aka gudanar da muhawarar.

Waɗannan abubuwa da za ku karanta ba su ne baki ɗayan abubuwan da suka faru yayin muƙabalar ba. Kuna iya shiga wannan shafin domin samun ƙarin bayani.

Sharuɗan da aka ce za a yi amfani da su yayin gudanar da muƙabalar

Kafin tsunduma cikin muhawarar gadangadan, alƙalin muƙabala Farfesa Salisu Shehu - shugaban cibiyar Musulunci da tattaunawa tsakanin addinai ta Jami'ar Bayero - ya bayyana sharuɗa kamar haka:

 • Za a gabatar da muƙabalar da Hausa
 • Za a bai wa dukkan ɓangarorin dama ba tare da fifita wani ba
 • Za a bai wa kowane bangare minti 10
 • Dukkan maudu'i suna da minti 30 tare da bayar da min 5 na ɗauraya
 • Za a bayar da dama na minti 5 na nuna hoto ko bidiyo ko sauti
 • Ba a yarda masu muƙabala su katse ɗaya daga cikinsu ba yayin da yake magana har sai lokacin da aka bayar ya cika
 • Ana buƙatar hujjoji ingantattu kuma karɓaɓbu a Musulunci
 • Dolo ne dukkan masu muƙabalar su kiyaye cakuɗa hadisai da ayoyi, a gabatar da su cikin ladabi
 • Dole ne a girmama juna tare da yin amfani da lafazi na mutuntawa
 • Babu zuga babu kirari, ko wani abu da zai nuna ɓangaranci

Malaman da suka fafata a mubaƙalar

Malaman da suka fafata a muƙabala

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fuskanci malamai huɗu ne yayin muƙabalar domin kare kansa daga zargin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.

 • Malam Mas'ud Mas'ud Hotoro daga ɓangaren ɗariƙar Ƙadiriyya kuma tsohon ɗalibin Sheikh Abduljabbar
 • Malam Abubakar Mai Madatai daga ɓangaren Tijjaniyya
 • Mallam Kabir Bashir Kofar Wambai daga ɓangaren ƙungiyar Izala
 • Dr. Muhammad Rabiu Umar Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya

Ba zan tuba ba - Sheikh Abduljabbar

Abduljabbar Nasiru Kabara

Shehin malami Abduljabbar Nasiru Kabara wanda shi ne mai kare kansa daga malamai huɗu da ke zargin da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, ya ce ba zai tuba ba a wurin wannan muƙabala "saboda rashin ƙwararan hujjoji".

Ya faɗi hakan ne a daidai loacin da Mallam Abubakar Madatai ya ce duk wanda ya ci mutuncin Annabi hukuncinsa kisa ne sannan ya nemi Abduljabbar da ya fito fili ya tuba.

Sai malamin ya ce: "Ba zan tuba a wurin wannan mukabala ba har sai an ba ni cikakkiyar hujja. Indai aka ba ni hujjojin da suka fi nawa zan tuba, amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan yana kan gaskiya. Ba'a biyo turbar da zan tuba ba."

Ina roƙon a sake yin muƙabala - Sheikh Abduljabbar

Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya roƙi 'yan uwan muhawararsa da gwamnatin Kano mai shirya muƙabalar da a asake zaman yin tattaunawa jim kaɗan bayan Mallam Abubakar Madatai ya tambaye shi game da cewa Annabi SAW ɗan giya ne.

Mallam Abubakar Madatai: "A wane hadisi ne ya zo cewa Annabi ɗan giya ne?; Lokacin da aka yi aurensa da Nana Khadija da a buge aka yi shi saboda sun sha giya; Annabi ya fito daga tsatson da ba tsarkakakke ba."

Abduljabbar: "Abu ne mai sauki; ji ne ko dai ma'anar ce ba a fahimta ba. Dukkan kalaman da ake tuhumata a kai kore su nake yi daga Annabi SAW. Ina roƙon a sake saka rana don sake tattaunawa da waɗan nan malamai don fito da abubuwa."

Minti 10 sun yi kaɗan wajen kwance litattafan da na zo da su - Abduljabbar

Sheikh Abduljabbar ya ce shi ma Annabi yake karewa daga irin ƙagen da ake yi masa a wasu hadisai amma babu isasshen lokaci na tabbatar da hakan "saboda minti 10 sun yi kaɗan".

"Abin da nake yi nake yi ina yin su ne don rarrabe hadisan da ake yi wa Annabi ƙarya. Da don Annabi ake yi da an bayar da isasshen lokaci don a yi muƙabalar. Littafan da na zo da su, minti goma sun yi kaɗan a kwance su.

Abduljabbar na fakewa da rashin lokaci ya ƙi amsa tambaya - Alƙalin muƙabala

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Farfesa Salisu Shehu
Bayanan hoto,

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Farfesa Salisu Shehu alƙalin muƙabala Farfesa Salisu Shehu na Jami'ar Bayero

Farfesa Salisu Shehu wanda shi ne alƙalin muƙabalar, ya zargi Sheikh Abduljabbar da ƙin amsa wasu tambayoyi da kuma ƙin buɗa littafi don bayyana inda ya ciro wasu abubuwan yana amai fakewa da rashin isasshen lokaci.

"A kowace gaɓa, malam Abduljabbar ba ya tsayawa a kan tambayoyin da aka gabatar masa saboda na farko yana cewa babu isasshen lokaci," a cewarsa.

"Na biyu yana cewa a tsaya a kan maudu'i ɗaya a yi magana, amma shi ne ba ya tsayawa a kan maudu'i guda ɗayan, sai ya yi ta yawo yana haɗo mas'aloli daban-daban maimakon ya yi bayani game da tambayoyin da aka yi masa.

"Idan ya yi da'awar cewa maganar da ya yi ta kaza a littafi kaza ya gani; in an ce ya buɗa littafi ya karanto wa mutane sai ya bayar da uzurin cewa babu lokacin da zai karanto wa mutane."

Alƙalin muƙabala na goyon bayan sauran malamai - Abduljabbar

Shehin malami Abduljabbar ya zargi alƙalin da ke kula da muhawarar, Farfesa Salisu Shehu, da cewa yana mara wa abokan muhawarar tasa baya.

"Kamata ya yi a ce a haɗaa ni da wanda na sani amma sai ga shi na ga alƙalin muƙabalar ya goyi bayan malaman da mukke mukabala da su," in ji shi.

Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da Mallam Kabir Bashir ya zarge shi cewa ya ce Annabi ya tura kawaliya don ta duba masa wata budurwa, zargin da Abduljabbar ya musanta nan take.

Abduljabbar ya ƙi bayar da amsar wata tambaya

Mallam Abduljabbar ya ƙi bai wa Malam Kabir Bashir Kofar Wambai amsar wata tambaya yana mai cewa ba a yi masa adalci ba; saboda ba a ba shi damar da zai kunna murya ba kamar yadda abokan muƙabalarsa suke yi.

Ya ƙara da cewa ba zai sake amsa wata tambaya kan wata muryarsa da aka kunna ba sai dai waɗanda aka kai wa gwamna da sarki waɗanda suka yi amfani da su a matsayin hujjar da kotu ta rufe masallacinsa kuma aka hana shi wa'azi.

Ban gamsu da muƙabalar ba - Abduljabbar

Jim kaɗan bayan kammala muhawarar ce kuma Sheikh Abduljabbar ya ce bai gamsu da muƙabalar ba amma ya ce duk sanda aka sake nemansa zai zo.

"Fisabilillahi da gyara, wannan ba tsarin yadda ake tsarin muƙabala ba ne, ban gamsu ba," in ji shi.

Ban san da tsarin muƙabalar ba sai da na zo nan - Abduljabbar

Shehin malamin ya ce ba a bayyana masa tsarin yadda muƙabalar za ta kasance ba har sai da ya shiga ɗakin tattaunawar.

"Matsalar ba su ba ni tsarin yin (muƙabalar) ba, ban san yaya za a gudanar ba balle na ba su shawarwari," a cewarsa.

"Fatanmu dai a samu nasara a zaman, a samu mafita ga wannan addini namu. Ba ƙure ce buƙatarmu ba; ina gaskiya take domin mu samar wa addininmu mafita."

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN