Ababe 8 da ya kamata ku sani kafin Layya na 6 zai kwantar maka da hankali


Imam Muhktar Abdullahi Walin Gwandu, Limamin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi, ya kara haske dangane da abin da ya kamata a sani lokacin Layya.

1. Ana Layya da Rakuma,Shanu, Tumaki da Awaki.

2. Ana Layya da tumaki da suka shekara daya.

3. Ana Layya da Awaki da suka shekara daya suka shiga ta biyu.

4. Ana Layya da shanu da ya cika shekara biyu ya shiga ta uku.

5. Ana Layya da Rakumi da ya shekara biyar ya shiga ta shida.

6. Tunkiya ko akuya na isamma mutum daya da iyalinsa.

7. Ya halalta mutum goma su yanke Rakumi data.

8. Ya halalta mutum bakwai su yanke shanu daya. Sa ko saniya.


Ababe da basa halalta a yi Layya da su.

1. Dabba mai ido daya.

2. Dabba da ke da bayyanannen rashin lafiya.

3. Dabba mai gurmunta.

4. Busassar dabba ko ramamma.


Ababen da ya kamata a kula

1. Kada a yanka dabbar Layya sai bayan an yi Sallar Idi.

2. Ba a rage gashin jiki ko aski ga mai niyyar yin Layya matukar watan Dhul-hijjah ya kama.

3. Ana son mai Layya ya yanke dabbarsa da kansa. Amma idan ba zai iya ba, ya halalta ya sami wani ya yanka masa sai ya biyashi.

4. Ba a sayar da nama, fata, ko wani abu daga cikin naman dabbar Layya.

Allah ya taimake mu ya karbi ibadarmu.

Ayi Sallah lafiya. 

Daukar nauyi:

Rt. Hon. Hassana Muhammad Shallah.
Alhaji Ibrahim Bagudu

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN