Yadda matasa suka kona tayoyi suka tare ayarin Gwamnan Kebbi a garin Ribah, gaskiyar lamari


Jami'an tsaro da ke tare da Gawamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu sun tarwatsa matasa masu zanga zanga bayan sun sa tayayin mota a kan titi suka kona su, sakamakon haka suka tare wa ayarin Gwamna hanyar wucewa ranar Asabar a garin Ribah.

Gwamna Bagudu yana kan hanyarsa ta zuwa yi wa jama'a da yan bindigan daji suka kashe yan'uwansu sakamakon hari da suka kai wasu kauyuka a kamarar hukumar Danko-Wasagu ranar Alhamis.

Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa matasan sun kona tayoyin ne daga wajen garin Ribah kan hanyar garin Waje. Wannan lamari ya sa jami'an tsaro da ke tare da Gwamna suka fito daga motocinsu domin su kori matasan.


Sai dai lokacin da jami'an tsaro suka fito sai matasan suka fara jifan su da duwatsu. Mun kuma samo cewa jami'an tsaron sun yi nassarar korar yaran kuma ayarin motocin Gwamna suka wuce.

Ana zargin cewa matasan sun kona wata motar yansanda wanda ta lalace, ba a amfani da ita, kuma aka barta a gefen titi

Mun samo daga majiya mai karfi kan harkar tsaro a jihar Kebbi cewa, jami'an tsaro da ke tare da Gwamna basu harbi kowa ba, kazalika basu kama kowa ba a wannan lamari a yau kawo yanzu. 


Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa tun farko, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya je Masarautar Zuru ne daga Abuja da jirgin Sanata Bala Ib'n Na'Allah domin ya yi jaje ga yan'uwan wadanda yan bindigan suka kashe a kauyukan karamar hukumar Danko-Wasagu ranar Alhamis. Kuma har ya koma lafiya kalau.

Majiyar tsaron a jihar Kebbi, ta ce " Gwamna baya da sojoji ko yansanda nashi na kanshi a jihar Kebbi, shi ma sai ya nemi manyan jami'an tsaro su kawo agaji a kan matsalolin tsaro a jiharsa ".

Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa babu jami'in tsaro da ya rasa ransa ko cikin matasa da suka kona taya a hatsaniyar ta yau. Babu wata motar ayarin Gwamna da aka kona ko aka lalata. Ba a harbi ayarin motocin Gwamna da bindiga ba kuma Gwamna Bagudu ya bar Masarautar Zuru lafiya, ya kuma isa masaukinsa lafiya.

Rahotun, Yahaya Muhammad, Kabiru Aminu, Deborah Yohana da Mawallafi Isyaku Garba Zuru.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN