Yadda PDP Ta Mulki Jihohi 31 Shekaru 14 da Suka Gabata da Yadda APC ta Kwacesu


A shekarar 2007, PDP ta yi mulki a duk fadin kasar kuma ta yi alfahari da cewa ita ce
 "jam'iyya mafi girma a Afirka". Ta kuma yi alfaharin cewa za ta mulki kasar na tsawon shekaru 60, in ji jaridar TheCable.

Ya zuwa ranar 30 ga Mayun 2007, PDP tana da jihohi 31 a karkashin ikonta.

Jihohin sun hada da Abia, Adamawa, Anambra, Akwa Ibom, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Ribers, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Yayin da rusasshiyar jam'iyyar ANPP ke da jihohin Yobe, Kano, Bauchi, da Borno, ita kuma rusasshiyar jam'iyyar AC tana da Legas.

Kotu daga baya ta tsige Andy Uba na PDP a matsayin gwamnan jihar Anambra, kuma wannan ya share fagen fitowar Peter Obi wanda ke dan jam'iyyar APGA ne a lokacin.

A yanzu APC ce mai rike da yawan jihohin Najeriya

Sai dai, a yanzu idan aka koma baya ga sauyin shekar da aka yi, a halin yanzu jam'iyyar APC ce ke rike da mafi yawan jihohin kasar.

Jam’iyyar mai mulki tana da jihohi 22, jam'iyyar adawa ta PDP na da jihohi 13 yayin da APGA ke rike da jiha daya tak.

A yanzu haka, jihohi 13 da ke karkashin babbar jam’iyyar adawar (PDP) sun hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Bayelsa, Benue, Delta, Edo, Enugu, Oyo, Ribas, Sokoto da Taraba.

APC, a daya bangaren, tana rike da Borno, Cross River, Ebonyi, Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Plateau, Yobe da baya-bayan nan Zamfara.

Zaben gwamnan Anambra da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba zai nuna ko PDP za ta iya dawo da asarar da ta yi ta hanyar karbe jihar daga APGA.

Yawan ku Ba Zai Hana Mu Karbar Mulki a 2023 Ba, PDP Ta Caccaki Gwamnonin APC

A wani rahoton na daban, Jam’iyyar PDP ta ce ba ta damu da sauya shekar da gwamnoni a karkashin jam’iyyar suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba, tana mai cewa tana da kyakkyawan shiri na karbe kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Gwamna Bello Mattawalle na jihar Zamfara a hukumance ya koma APC daga PDP a ranar Talata, ya zama gwamna na biyu da ya bar babbar jam’iyyar adawar zuwa jam’iyya mai mulki bayan wata daya kacal da takwaransa na jihar Kuros Riba Ben Ayade ya koma APC.

Amma PDP ta nace cewa ficewar ba wani abin damuwa ba ne, tana mai cewa APC ba ta cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya ba, Channels Tv ta ruwaito.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN