Maigida ya yi wa matarsa mai yara 3 dukan ajali domin ta ki ara mashi N2000


Ana zargin wani magidanci mai suna Christopher mai shekara 45 a Duniya ya yi wa matarsa yar shekara 39 a Duniya mai suna Isoken kuma mahaifiyar yara 3 duka har ta mutu saboda ta ki ranta masa N2000 Vanguard ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da dare a gida mai lamba No 1, Agbontaen Street, a gefen makarantar sakandare ta Ebvareke, a Unguwar Agboniro , da ke Uselu,  a garin Benin.

Wani dansu Dan shekara 13 mai suna Augustine wanda ya gan lokacin da lamarin ya faru, ya ce mahaifinsa ya kira mahaifiyarsa a wayar salula ya tambaye ta cewa ta ara mashi N2000 amma ta ki.

Ya ce bayan mahaifinsa ya dawo gida da misalin karfe 9 na dare, sai ya fara dukan mahaifiyarsa cewa tana wulakanta shi duk lokacin da ya nemi rancen kudi a wajenta.

Ya ce mahaifiyarsa ta nemi Agustine ya bata ruwa da magani Paracetamol, amma sai mahaifinsa ya watsar da maganin.

Daga bisani mahaifiyarsu wacce take zaune a waje ta yanke jiki ta fadi. Amma sai mahaifinsu ya rufe yaran su 3 a cikin daki ya je ya sami uwarsu da ta fadi a kasa ya ci gaba da dukanta.

Daga bisani makwabta suka kawo dauki sakamakon hayaniya ta suka jiyo daga gidan, inda suka tarar da mahaifiyar Agustine kwance bata motsi. Sakamakon haka suka kaita Asibiti har guda biyu inda Likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Agustine ya ce mahaifinsu ya dade yana dukan mahaifiyarsu duk lokacin da suka sami yar matsala. Ya kara da cewa mahaifinsu dan wiwi ne kuma yana matukar kwankwadar barasa.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN