Maigida ya kwade amarya da tabarya a kai, ya gundule kanta a jihar Kebbi


Wani magidanci a wata ruga da ke kauyen Zuttu a Gundumar kasar Kanya da ke karamar hukumar Danko wasagu a jihar Kebbi ya kashe kansa bayan ya kashe amaryarsa cikin dare ranar Alhamis. Gidan ridiyon vision ta labarta.

Rahotannin da wakilin gidan rediyon Muhammad Yazeed ya tattaro, sun samar da muryar wani ganau da bayason a ambaci sunansa, ya ce mijin Yana zargin matarsa ne da bin maza.

Sakamakon haka ya yi kokarin hanata amma ta ki. Cikin daren ranar Alhamis, mijin ya sameta tana barci ya maketa da tabarya daga bisani ya gundule kanta ta hanyar yi mata yankan rago har Kai ya rabu da fatar jiki.

Rahotun ya nuna cewa bayan ganin hakikanin abin da ya aikata. Sai mijin ya je ya rataye kanshi a wata itaciya da ke gefen gari.

Kazalika rahotun ya ce wani dansa karamin yaro da ya gan abin da ya faru ne ya je ya gaya wa mutane halin da ya gan mahaifinsa.  Rahotun ya kuma ce yansanda sun je wajen da larin ya faru kuma sun dauke gawakin guda biyu daga rugar. 


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN