Fitaccen dan siyasan Najeriya, Dino Melaye yayi fice wurin kaunar manyan motocin alfarma da kuma kudin da ya narka duk don kawata garejinsa.
Amma kuma babu wanda ya taba tsammanin cewa akwai wanda zai yi wa tsohon sanatan fallasa kan bashi.
A cikin kwanakin nan ne wani dillalin motoci a Instagram mai suna Unique Motors, yayi kira ga tsohon sanatan tare da yin ikirarin cewa yana bin shi wasu kudi na motar da ya siya.
A wata wallafa da Unique Motors tayi a labarinta na Instagram, sun wallafa hoton Dino tsaye kusa da wata mota kirar Mercedes Benz SUV wacce tuni dan siyasan yasa lambarsa a jikinta, sun yi ikirarin cewa bai biya ragowar kudin motar ba tun 2019.
Kamar yadda Unique Motors suka wallafa, suna son kawai ya biya su ragowar kudin mota da ya dauka.
Jama'a sun yi martani
Wasu ma'abota amfani da kafar sada zumuntar sun yi kira ga tsohon sanatan kuma sun yi martani.
Corpersdiary_ng cewa yayi: " Kai kai! Ina fatan wannan zargin ya zama karya ko kuma mu fara yi wa sanatan ba'a."
_Ava.officiall cewa tayi: "Dalilin da yasa bana yadda da duk abinda na gani a Instagram. Duk karya ce."
Ogechukwukama cewa yayi: "Ku kai shi kotu mana kuma ku daina damunmu."
A wani labari na daban, sauran shekaru biyu zabe amma akwai manyan kalubale dake kokarin tarwatsa jam'iyyar APC a jihar Kano, babbar cibiyar kasuwancin arewa kuma jihar da jam'iyyar ke takama da kuri'unta.
Manyan matsalolin da suka samu zama a babbar cibiyar kasuwancin arewan zasu iya zama kalubale ga jam'iyyar a fadin Najeriya saboda yawan kuri'un da ake samu daga jihar.
Matsalolin sun fara bayyana ne a ranar Laraba biyo bayan sanarwar dakatarwa da aka yi wa dan majalisa mai wakiltar birnin Kano a majalisar wakilai, Sha'aban Ibrahim Sharada.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari