An sami wata yar dirama a Zauren Majalisar kasar Tanzania yayin da aka umarci wata yar Majalisa ta fice daga Zauren Majalisar saboda ta sa matsatsen wando ta shigo Majalisar.
Yar Majalisar mai wakiltar Momba mai suna Condester Sichwale, ta fuskanci kalubale ne a Zauren Majalisar bayan wani dan Majalisa ya koka kan yanayin sutura da ta sa ta shigo Zauren Majalisar.
Daga bisani shugaban Majalisar ya umarci yar Majalisar cewa ta fita daga Zauren Majalisar saboda matsatsen wando da ta saka.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari